11 Afirilu 2020 - 05:14
​Iran:Za’a Fara Amfani Da Tsarin Jinyan Cutar Corona Na Plasma A cikin Makonni Masu Zuwa

Likitoci a nan kasar Iran zasu fara amfani da tsarin jiyar wadanda suke kamu da cutar Corona wanda ake kira “Palasma” ko kuma jinin wadanda suka warke daga cutar.

(ABNA24.com) Likitoci a nan kasar Iran zasu fara amfani da tsarin jiyar wadanda suke kamu da cutar Corona wanda ake kira “Palasma” ko kuma jinin wadanda suka warke daga cutar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Nasir Rayyahi mamba a kwamitin kwararru a nan tehran yana fadin haka. Ya kuma kara da cewa jinyan cutar Corona ta hanyar amfani da bangaren jinin wadanda suka warke daga cutar, ya yi amfani sosai a cikin gwaje-gwajen da suka gudanar a yan kwanakin da suka gabata.

Rayyahi ya kara da cewa a halin yanzu za su ware mutane 200 dauke da cutar ta Corona, sannan a yi masu alluran Palasma na jinin wadanda suka warke daga cutar, idan an har an sami sakamako mai kyau a wannan gwajin na karshe, ta za su fara amfani da tsarin jinya a duk fadin kasar.

Har’ila yau za su buga sakamakon gwajin da suka yi, a wata mujallar kiwon lafiya ta kasa da kasa, don sauran kasashen duniya ma su amfana da tsarin.


/129