(ABNA24.com) Wata sanarwa da ma’aikatar lafiyar kasar ta fitar ta ce ye zuwa ranar 1 ga watan Afrilu Mutum 74 ne aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus, Daga cikinsu akwai biyu da aka gano a jihar Maradi karon farko.
A yanzu dai mutum 69 ne ke jinyar cutar, a fadin kasar inji sanarwar, yayin da adadin wandanda cutar ta kashe ya karu zuwa 5.
A sanarwar da ministan lafiya na kasar Dakta Illiasu Idi Mai Nasara ya sanya wa hannu ya bukaci jama’a dasu kiyaye sosai matakan da aka gindaya domin kaucewa kamuwa da cutar.
342