31 Maris 2020 - 16:09
​Najeriya: Hukumar NCDC Na Ci Gaba Da Kokarin Gano Wadanda Suka Kamu Da Corona

Hukumomin kiwon lafiya a Najeriya sun ce sun dukufa wajen ganin an gano wadanda suka kamu da cutar corona a kasar, ta hanyar tantance mutanen da suka yi mu’amala da masu dauke da cutar.

(ABNA24.com) Rahotannin da hukumar NCDC ta bayar a jiya dai sun ce adadin wadanda suka kamu da cutar ya karu zuwa 111, kuma akwai yiwuwar adadin ya ci gaba da karuwa, matukar aka gao wadanda suka yi mu’amala da masu dauke da cutar a cikin fadin kasar.

Yanzu haka dai Jihar Legas na da mutum 68 da suka kamu da cutar, sai Abuja 21, Ogun 3, Oyo 7, Enugu, Edo da Bauchi, bibbiyu, Ekiti, Benuwai daya, Osun 2, Ribas 1, Kaduna 1.

Akwai wasu kasashe a nahiyar Afirka, da har yanzu ba a samu wadanda suka kamu da cutar ba.

Daga cikin kasashen akwai Bostwana, Burundi, Lesotho, Malawi, da sauransu, wadanda har yanzu ba a samu wadanda suke dauke da cutar a cikin kasashen ba.

342