(ABNA24.com) A wata sanarwa da Hukumar NCDC mai fada da yaduwar cututtuka a kasar ta fitar a shafinta na Twitter ta ce ya zuwa karfe 9 na daren jiya Litinin adadin wadanda suka kamu da cutar ta COVID-19 sun kai 131 bayan an samu karin wasu mutane 20 da suka kamu da cutar.
Har ila yau sanarwar ta kara da cewa wani mutum kuma da ke dauke da cutar ya mutu wanda hakan ya sanya ya zuwa yanzu mutanen da suka mutu a Nijeriya din sakamakon cutar ya kai mutane biyu kenan.
Hukumar NCDC din ta ci gaba da cewa mutane 20 din da suka kamu da cutar sun fito ne daga jihohi uku da kuma babban birnin kasar wato Abuja tana mai cewa mutane 13 daga Lagos, 4 daga Abuja, 2 daga Kaduna da kuma mutum guda da jihar Oyo.
342