(ABNA24.com) Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon sayyid Hassan Nasarallah ya yaba da yadda gwamnatin kasar ta Lebanon take aiwatar da yakar cutar Corona a kasar.
Tashar talabijin ta Almanar ta nakalto Sayyid Nasaralla yana fadar haka a jiya da yamma, inda ya bukaci dukkanin mutane su bada hadin kai don yakar wannan cutar.
A wani bangare kuma sayyid Nasarallah ya yaba wa shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yeman don shirinsa na musayar fursinonin Saudiyya da suke hannunsa da kuma Palasdinawa da aka tsare a kasar ta Saudiyya.
/129
30 Maris 2020 - 07:13
Lambar labari: 1021688
Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon sayyid Hassan Nasarallah ya yaba da yadda gwamnatin kasar ta Lebanon take aiwatar da yakar cutar Corona a kasar.