22 Maris 2020 - 13:00
Nijeriya Za Ta Rufe Sauran Manyan Filayen Jiragen Samanta Saboda Coronavirus

A ci gaba da ƙoƙarin daƙile cutar nan ta Coronavirus a ƙasar, gwamnatin Nijeriya ta sanar da cewa daga gobe Litinin za ta dakatar da dukkanin saukar jiragen sama daga wajen ƙasar a manyan filayen jiragen saman ƙasar biyu da suke Abuja da Lagos.

(ABNA24.com) Babban daraktan Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya NCAA Musa Nuhu ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce: Daga ranar 23 ga watan Maris har zuwa 23 ga watan Afprilu za a rufe filayen jiragen sama na Murtala Muhammed International Airport da ke Lagos da kuma Nnamdi Azikiwe International Airport) da ke Abuja daga saukar jirage daga kasashen waje.

Kafin hakan dai hukumar ta sanar da daukar irin wannan matakin kan wasu manyan filayen jiragen saman kasar guda uku, wato filin Malam Aminu Kano International Airport, Kano; Akanu Ibiam International Airport, Enugu; da kuma Port-Harcourt International Airport.

Ita ma a nata bangaren hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Nijeriyan ta sanar da dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a fadin kasar daga gobe Litinin domin dakile yaduwar cutar ta Covid-19 a kasar.

Wadannan matakan suna zuwa ne a daidai lokacin da aka samun karin wasu mutane da suka kamu da cutar ta Coronavirus a Nijeriyan.

342