(ABNA24.com) Ministan harkokin tsaron kasar Turkiyya Hulusi Akar ya sanar da cewa Turkiyya da Rasha zasu kafa cibiyoyin hadin gwiwa a yankin Idlib na Siriya.
M.Hulusi ya bayyana hakan ne bayan tattaunawar da aka yi da tawagar sojojin kasar Rasha a Ankara babban birnin Turkiyya, Inda ya ce dukkanin bangarorin biyu sun rattaba hannu akan matsayar da aka cimma.
Ministan, ya kara da cewa za'a kafa cibiyoyin kulawar ne tare da haddin gwiwa da Rasha kuma dukkanin kasashen biyu zasu kasance masu sanya ido a cibiyoyin, sannan kuma babbar bukatar Turkiyya ita ce a tsagaita wuta mai dorewa a yankin na Idlib.
Ya kara da cewa irin wannan matakan ne zasu hana al'umman Idlib ficewa daga matsugunansu dama sanya komawar wadanda suka yi hijira gidajensu.
/129
15 Maris 2020 - 06:43
Lambar labari: 1017535
Ministan harkokin tsaron kasar Turkiyya Hulusi Akar ya sanar da cewa Turkiyya da Rasha zasu kafa cibiyoyin hadin gwiwa a yankin Idlib na Siriya.