7 Maris 2020 - 06:44
Assad: Babu Kyautata Alaƙa Da Turkiya Sai Erdogan Ya Daina Taimkon ‘Yan Ta’adda

Shugaban ƙasar Siriya Bashar al-Assad ya kore yiyuwar kyautata alaƙa da ƙasar Turkiya nan kusa yana mai cewa hakan ba abu ne mai yiyuwa ba matuƙar dai shugaban Turkiyyan Recep Tayyip Erdogan ya ci gaba da goyon bayan ƙungiyoyin ta’addancin da yake yi a ƙasar Siriya.

(ABNA24.com) Shugaban ƙasar Siriya Bashar al-Assad ya kore yiyuwar kyautata alaƙa da ƙasar Turkiya nan kusa yana mai cewa hakan ba abu ne mai yiyuwa ba matuƙar dai shugaban Turkiyyan Recep Tayyip Erdogan ya ci gaba da goyon bayan ƙungiyoyin ta’addancin da yake yi a ƙasar Siriya.

Shugaba Assad ya bayyana hakan ne cikin wata hira da yayi da tashar talabijin ɗin ƙasar Rasha Rossiya 24 inda ya ce: Erdogan yana yaƙi tare da ‘yan ta’adda ne don cutar da ƙasar Siriya sakamakon aƙidarsa ta Muslim Brotherhood. Don haka shi da kansa ya gagara gaya wa al’ummar ƙasarsa dalilin da ya sanya shi tura sojojin ƙasar zuwa Siriya. Dalilin dai shi ne wannan aƙida tasa ta Muslim Brotherhood.

Shugaba Assad ya ce babu wani abin da al’ummar Siriya suka yi wa Erdogan da suka cancanci irin wannan cutarwar da yake musu yana mai cewa: Lalle babu wata maganar ƙulla alaƙa tsakanin Siriya da gwamnatin Erdogan matuƙar dai bai daina goyon bayan ‘yan ta’adda ba.

Cikin ‘yan kwanakin nan dai rikici ya sake ɓarkewa tsakanin sojojin ƙasashen biyu sakamakon irin goyon bayan da gwamnatin Erdogan ɗin take ba wa ƙungiyoyin ‘yan ta’adda da suke yaƙar gwamnatin Siriyan a lardin Idlib a ƙoƙarin da gwamnatin take yi na tsarkake lardin daga ‘yan ta’addan.




/129