(ABNA24.com) Minsitan harkokin wajen kasar Iran, Mohammad Javad Zarif, ya yaba wa hukumar lafiya ta duniya (WHO), a kokarin da take na taimaka wa kasar da kayan aiki da kuma kwararun likitoci a yakin da take da cutar coronavirus.
M. Zarif, ya fada a shafinsa na twitter cewa muna godiya ga WHO, da kuma kasashe amminai da suke taimakwa a yaki da # COVID19, duk da takunkuman ta’addancin Amurka kan tattalin arziki, wanda je jefa rayuwar Iraniyawa marasa lafiya cikin hatsari.
A daya bangaren kuma, ministan harkokin wajen kasar ta Iran, ya isar da godiya ga kasashe amminan kasarsa kan anniyarsu ta taimaka wa kasar a yaki da cutar.
Baya ga kasashen Rasha da kuma China, a baya baya nan kasahen Biritaniya, Jamus da kuma faransa, sun ce zasu aike wa da kayan aiki na yaki da cutar da kuma tallafin kudi dala Miliyan 5,6 ga hukumar lafiya ta duniya da kuma kungiyoyin agaji domin taimakawa da kayayakin da ake bukata na yaki da cutar.
/129
4 Maris 2020 - 08:17
Lambar labari: 1014729
Minsitan harkokin wajen kasar Iran, Mohammad Javad Zarif, ya yaba wa hukumar lafiya ta duniya (WHO), a kokarin da take na taimaka wa kasar da kayan aiki da kuma kwararun likitoci a yakin da take da cutar coronavirus.