2 Maris 2020 - 07:39
Najeriya : Buhari Ya Bukaci Jama'a Su Daina Tayar Da Hankali Game Da Coronavirus

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan kasar su daina tara da hankali game da bullar cutar cutar coronavirus a kasar.

(ABNA24.com) Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan kasar su daina tara da hankali game da bullar cutar cutar coronavirus a kasar.

Wannan dai shi ne karon farko da shugaba Buharin, ya yi magana tun bayan bullar cutar a kasar.

Buhari ya kuma yaba wa ma'aikatar lafiyar kasar da Hukumar Hana Yaduwar Cututtka, NCDC da gwamnatocin jihohin Legas da Ogun bisa matakan da suka yi gaggawar dauka a kan cutar.

Shugaban kasar ya kuma yi kiraga ‘yan kasar dasu da su bi matakan kariya da ma'aikatun Lafiya da hukumar Lafiya ta Duniya, WHO da NCDC suka bayar domin kare kawunansu daga kamuwa da coronavirus.

Sakon shugaban na zuwa ne 'yan sa'o'i bayan wasu 'yan kasar sun yi ca a kan mai magana da yawunsa kan wani sako da ya wallafa a Twitter, inda ya zargi jaridun kasar da rashin mayar da hankali kan mace-macen da ke samu a kasar ta dalilin zazzabin cizon sauro.




/129