(ABNA24.com) Shugaban kasar Afgasnitan, Ashraf Ghani, ya yi watsi da daya daga cikin mahimmin batun da ya shafi yarjejeniyar zaman lafiyan da Amurka ta cimma da kungiyar Taliban.
Wannan dai a cewar masana wata manuniya ce ta cewa akwai matukar wuya gwamnatin ta Kabul da ‘yan Taliban sun cimma sulhu a tsakaninsu.
Gwamnatin Afganistan wacce aka ware ta daga tattaunawar ta tsakanin Amurka da kungiyar ta Taliban, ta ki amince musayar fursunoni 5,000 da jami’an tsaro 1,000 da ‘yan Taliban din ke tsare da kamar yadda yarjejeniyar ta tanada.
Shugaban kasar ta Afganistan ya bayyana cewa Amurka ba ta da hurimin yanke shawara kan irin wannan matakin, kuma a cewarsa idan har Amurka ta nace kan hakan, to tattaunawar ba ta da wata fa’ida.
A ranar Asabar data gabata ce Amurka da kungiyar ta Taliban suka cimma yarjejeniyar ta zaman lafiya wacce Amurka ta danganta da mai cike da tarihi, wacce kuma ta tanadi janyewar sojojin Amurka daga kasar ta Afganistan a cikin watanni 14 masu zuwa.
/129