24 Faburairu 2020 - 05:10
​Iran: Adadin Wadanda Suka Kada Kuri’a Ya Kai Kashi 42.57

Ma’ikatar harkokin cikin gida akasar Iran ta sanar da cewa, adadin wadanda suka kada kuriunsu a zaben ‘yan majalisar dokokin kasar da kuma ‘yan majalisar kwararru da ka gudanar a ranar Juma’a da ta gabata.

(ABNA24.com) Ma’ikatar harkokin cikin gida akasar Iran ta sanar da cewa, adadin wadanda suka kada kuriunsu a zaben ‘yan majalisar dokokin kasar da kuma ‘yan majalisar kwararru da ka gudanar a ranar Juma’a da ta gabata.

Ministan harkokin cikin gida a kasar Iran Abdulrida Fadli ya sanar da cewa, bisa kididdigar karshe da ak agudanar, adadin mutanen da suka kada kuri’unsu a zaben ranar Juma’a ya kai kasha 42.57 na daga adadin mutanen da suka cancanci kada kuri’a.

Wannan dai shi ne karo na 11 da ake gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki akasar Iran tun bayan samun nasarar juyin juya halin muslunci a kasar a shekra ra 1979.

Jami’an ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Iran sun bayyana cewa, wasu daga cikin mutanen kasar ba su halarci wuraren zabukan ne ba saboda tsoron kamuwa da cutar Coronavirus, wadda ta bulla a kasar, inda ake da tabbacin cewa mutane 18 sun kamu da ita a kasar, kuma 8 daga cikinsu sun mutu.


/129