(ABNA24.com) Tashar talabijin ta Al-alam ta bayyana cewa, a ziyarar da shugaban majalisar dokokin kasar Iran yake gudanarwa a Lebanon, ya gana da manyan jami’an gwamnatin kasar, da suka hada da shugaban kasar Micheal Aoun, da kuma shugaban majalisar dokoki Nabih Birri, gami da Firayi ministan kasar Hassan Diyab.
Haka nan kuma Larijani ya gana da babban sakataren kungiyar Hizbullah sayyid Hassan Nasrullah, a ganawarsa da Sayyid Nasarallah, bangarorin biyu sun tattauna matsalolin yankin gabas ta tsakiya da kuma hanyoyin fuskantar su.
A daya bangaren kuma Larijani ya gana da shugaban kungiyar Jihadul Islami ta Falastinu Ziyad Nakhala, inda suka tattauna batutuwa da suka shafi halin da ake ciki a Falastinu.
Baya ga haka kuma Larijani ya gana da wasu daga cikin wakilan kungiyoyin falastinawa daban-daban a birnin Beirut a jiya Litinin, inda a nan ma suka tattauna batun halin da ake ciki a falastinu da kuma batun yarjejeniyar karni.Har ila yau a jawabin da yayi wa yan jaridu Dr Larijani, ya bayyana kisan da Amurka ta yi wa Shahid Kasim Sulaimani a matsayin wata manuniya ta gazawa daga gwamnatin kasar ta Amurka.
Dangane da matsalolin siyasa da tattalin arzikin da sabuwar gwamnatin kasar Lebanon take fuskanta kuma, Larijani ya ce gwamnatin kasar Iran a shirye take ta taimaka don ganin an shawo matsalolin.
/129
18 Faburairu 2020 - 11:01
Lambar labari: 1011353
A ziyarar da yake yi a kasar Lebanon shugaban majalisar dokokin kasar Iran Dr Ali Larijani ya gana da manyan jami’an gwamnatin kasar Lebanon.