(ABNA24.com) Shugaban kwamitin zartarwa na kungiyar tarayyar Afrika ya bayyana cewa akwai manyan kalu bale a gaban gwamnatocin kasashen Afrika.
Musa Faki Muhammad ya bayyana hakan ne yau a gaban taron shugabannin kasashen Afrika abirnin Addis Ababa na kasar Habasha,inda ya ce kalu balen da Afrika take fuskanta ahalin yanzu hard a na barazanar ta’addanci, da kuma rikcin kasar Libya.
Ya ce kasashen Afrika na bukatar hada karfi da karfe a yanzu fiye da kowane lokaci domin fukantar muhimman abubuwan da suke a gabansu, domin tabbatar da cewa matsalolin da ake fuksnta a shawo gabansu, tare da mayar da hankali ga abubuwan da za su kara bunkasa nahiyar, ta fuskoki na tattalin arziki da kuma cinikayya.
Shi ma a nasa bangaren shugaban kasar Masar da yake gabatar da nasa jawabin a yau, ya bayyana cewa dole ne kasashen Afrika su zama masu karfin halin da za su iya warware matsalolinsu da kansu, ba tare da tsoma baki na kasashen ketare ba, inda ya bayar da misalign rikicin kasar Libya, wanda ya ce kasashen ketare ne suke da hannu wajen kara ruruta wutar rikicin na Libya.
Taron na shugabannin kasashen Afrika ya samu halartar shugabannin kasashe da kuma shugabannin gwamnatoci, da kuma manyan jami’ai na majalisar dinkin duniya da tarayyar turai da kuma kungiyar kasashen larabawa da kuma bankin duniya.
/129
12 Faburairu 2020 - 07:10
Lambar labari: 1009675
Shugaban kwamitin zartarwa na kungiyar tarayyar Afrika ya bayyana cewa akwai manyan kalu bale a gaban gwamnatocin kasashen Afrika.