20 Janairu 2020 - 19:57
​Jagora: Jajircewar Mutanen Iran Ne Ya Fusata Amurka

Jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullahi Sayyeed Aliyul Khamina’i ya bayyana cewa dagewar da mutanen kasar Iran suka yi kan bin tsarin musulunci wanda ya hada da hakuri da jajircewa kansa na daga cikin abubuwan da suka fusata Amurka sannan ya ja hankalin kasashen duniya da dama.

ABNA24-Jagoran ya bayyana haka ne a yau Litinin a lokacinda ya ke ganawa da jami’an hukumar Hajji da Umra ta kasar a gidansa. Ya kuma kara da cewa ayyukan hajji da umra al-amura ne na siyasa da kuma zamantakewa a addinin musulunci, sai dai abin bakinciki mafi yawan musulmi sun kasa gane hakan.

Jagoran ya ja hankalin jami’an hukumar da su bada karfi wajen wayar da kan sauran musulmi wadanda suke haduwa da su a wurare masu tsarki don wayar da kawukansu.

Daga karshe jagoran ya yi ishara kan hadin kan al-ummar musulmi ta duniya, da kuma yadda makiya suke iya kokarinsu na ganin haka bai tabbata ba. Don haka yana da matukar muhimmanci al-ummar musulmi su fahinci haka su kuma sani cewa musulunci cikekken tsari ne wanda bai da nakasa. Wannan yana daga cikin muhimman ayyukan Hajji da Umra, inji jagoran.