20 Janairu 2020 - 10:59
​Iran Ta Yi Kakkausar Suka Kan Hukuncin AFC

​Iran Ta Yi Kakkausar Suka Kan Hukuncin AFC

Taskar watsa labarai ta Ahlul-Baiti-ABNA24- ta rawaito Manyan kungiyoyin kwallon kafa guda hudu, kuma wakilan kasar Iran a hukumar wasannin kwallon kafa ta kasashen Asia wato “the Asian Football Confederation (AFC), sun maida martani kan hukuncin da hukumar ta yanke na haramtawa Iran daukar nauyin wasannin kwallon kafa na kakar wasanni na wannan shekara.

Kungiyoyin kwallon kafar guda hudu sun tabbatar da cewa ba za su taba amincewa da hukuncin na hukumar wasannin kwallon kafa ta kasashen Asia ba, kuma babu wata kungiyar kwallon kafa daga kasar Iran da zata shiga cikin wasannin da hukumar zata shirya a wannan kakar wasanni.

A jiya ne kwamitin shirya wasanni a hukumar wasannin ta AFC ya aike wa kungiyoin kwallon kafa na kasar Iran kan cewa kwamitin ba zai shirya wasanni a kasar Iran ba domin abin da ya kira rashin tsaro da kuma zaman lafiya a kasar.

A jiya Lahadi ne majalisar koli da hukumar wasannin kwallon kafa ta kasashen Asia ta tabbar da hukuncin kwamitin tsara wasannin na hukumar, wanda ya haramta wa Iran daukar bakoncin wasannin kwallon kafa na kakar wasanni a wannan shekara.