19 Janairu 2020 - 17:33
An Kai Sojojin Amurka 16 Da Suka Samu Munanan Raunuka Zuwa Asibitin Kuwait

An Kai Sojojin Amurka 16 Da Su ka Sami Munanan Raunuka A Aynul-Asad Zuwa Kasar Kuwaiti Domin Yi Musu Magani

Taskar watsa labarai ta Ahlul-Baiti-ABNA24- ta rawaito Jaridar Al Qqbs, ta Kasar Kuwaiti ta buga rahoton da yake cewa; kwanaki kadan da su ka gabata an kai wasu sojojin Amurka da su ka sami munanan raunuka sanadiyyar harin makamai masu linzami da Iran ta kai a sansanin sojan Amurka na Aynul Asad a kasar Iraki

Rahoton ya kara da cewa; Wasu daga cikin sojojin Amurkan sun sami munanan raunuka da su ka hada da konewa, wasu kuma da akwai baraguzan makaman da aka harba akan sansanin na Aynul Asad.

A shekaran jiya juma’a ma dai wasu majiyoyin na Amurka sun bayyana cewa; sojoji 11 ne na Amurkan su kajikkata a sanadiyyar harin na Iran.

Tun da fari Amurkan ta yi kokarin kore cewa sojojinta sun jikkata a sansanin soja na Aynul Asad da Iran ta kai wa harin daukar fansar kisan Janar Kassim Sulaimani