Taskar watsa labarai ta Ahlul-Baiti-ABNA24- ta nakalto ,Jaridar Vanguard da ake bugawa a Najeriya ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake zantawa da ‘yan Najeriya mazauna kasar Birtaniya a jiya a birnin Landan, shugaba Buhari ya bayyana dalilan da suka sanya gwamnatinsa ta dauki matakin rufe iyakokin kasar.
Shugaban ya ce manufar hakan ba ita ce cutar da kasashe da suke makwabtaka da Najeriya, domin kuwa ta hanyar rufe iyakokin Najeriya ta samu nasara wajen dakushe fasa-kwaurin kayayyakin abinci da kuma shigo da makamai.
Baya ga haka kuma ya ce, sakamakon rufe iyakokin manoma a Najeriya suna darawa, domin kuwa sun samu gagarumar riba wajen sayar da amfanin gonar da suke nomawa.
Ya ce bunkasa lamarin noma a Najeriya zai taimaka ma miliyoyin matasa da suke zaune babu aikin yi, domin su samu ingantacciyar rayuwa a gaba.