(ABNA24.com) Limamin masallacin Jumma’a a birnin Kermon kuma wakilin jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullahi Sayyeed Aliyul Khamina’e a lardin ya karanta jawabin jagoran a dai-dai lokacinda aka fara shirin jana’izar Shaheed Sulaimani da abokan shahadarsa a birnin Kerman a safiyar yau Talata.
Tashar talabijin ta Al-Alam a nan Tehran ta bayyana cewa Limamin ya karanta nassin ta’aziyan da jagoran ya rubuta jim kadan bayan shahadar Janar Kasim Sulaimani a daren jumma’an da ta gabata, Inda ya bayyana Shaheed Kasim Sulaimani a matsayin mutum wanda ya yi khidima wa masulmi a kasar Iran da kasashen yankin da dama. Kuma yana daga cikin wadanda suka yi karatun gwagwarmaya na son shahada a makarantar Imam Khumaini(q).
Daga karshe wakilin jagoran a Kerman ya bayyana cewa shaheed Kasim Sulaimani da kansa ne ya bar wasiya na cewa a yi masa sutura a mahaifarsa Kermon.
Har’ila yau a wani labarin kuma an bayyana cewa mutane dama ne suka rasa rayukansu a garin na Kerman saboda cinkoso na jama’a a jana’iar da akewa shaheed Sulaimani a garin na Kemon. Al-Alam ta ce, wannan ya sa aka jirkirta jana’izar zuwa wani lokacin don kubutar da rayukan mutane.
Mutanen garin kerman dai basu fi 700,000 ba, amma miliyoyin mutanen daga ciki da wajen kasar Iran ne suka shiga garin don halattar jana’iazar Shaheed Sulaimani.
/129
8 Janairu 2020 - 05:56
Lambar labari: 1000431
Limamin masallacin Jumma’a a birnin Kermon kuma wakilin jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullahi Sayyeed Aliyul Khamina’e a lardin ya karanta jawabin jagoran a dai-dai lokacinda aka fara shirin jana’izar Shaheed Sulaimani da abokan shahadarsa a birnin Kerman a safiyar yau Talata.