(ABNA24.com) Babbann sakataren majalisar tsaron kasa ta kasar Iran Ali Shamkhani ya bayyana cewa majalisarsa ta fidda matakai har guda 13 na daukar fansar kisan Shaheed Sulaimani kan sojojin Amurka, wanda mafi rauni daga cikinsu sai ta girgaza kasar ta Amurka.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto shamkhani ya na fadar haka a safiyar yau Talata. Babban sakataren majalisar tsaron ya kara da cewa tuni sun fidda sansanonin sojojin Amurka guda 19, daga ciki akwai manya-manya guda 11 wadanda suke gabas da kuma yammacin kasar ta Iran, inda suke lura da dukkan motsin da sojojin Amurka suke yi a cikinsu.
Daga karshe Shamkhani ya ce ba zai kara wani bayani fiye da haka ga kafafen watsa labarai ba. Amma ya kara jaddada cewa matukar sojojin Amurka basu fice daga yankin ba to kuma za’a rika maida gawakinsu gida Amurka.
/129
8 Janairu 2020 - 05:56
Lambar labari: 1000428
Babbann sakataren majalisar tsaron kasa ta kasar Iran Ali Shamkhani ya bayyana cewa majalisarsa ta fidda matakai har guda 13 na daukar fansar kisan Shaheed Sulaimani kan sojojin Amurka, wanda mafi rauni daga cikinsu sai ta girgaza kasar ta Amurka.