-
Qassam Sun Kai Munanan Hare-haren Kan Sojojin Isra'ila
Mummunan fashewar a Rafah ta faru ne akan Sojojin yahudawan sahyoniya wanda biyu daga ciki duka mutu nan take biyar suka jikkata 7
-
Yemen Ta Kai Hari A Filin Jirgin Saman Ramon Da Wani Muhimmin Wuri A Jaffa/Cikakkun Bayanai Na Faduwar Jirgin Yakin Amurka F-18
Dakarun kasar Yemen sun kai farmaki tashar jiragen sama na Ramon na Isra'ila da kuma jirgin Amurka Truman a wasu jerin hare-haren soji, kafin Amurka ta sanar da dakatar da kai hare-hare kan kasar Yemen.
-
Pakistan A Musayar Wuta Tsakaninta Da Indiya, Ta Tabbatar Da Kame Sojoji Da Kabo Jiragen Sama.
Kakakin rundunar sojin Pakistan na cewa, an tafka ruwan bama-bamai a wurare da dama na kan iyakar kasashen biyu, a yayin da hukumar ta ambato sojojin Indiya na cewa fararen hula 10 ne suka mutu yayin da wasu 35 suka jikkata a harin da Pakistan ta kai a yankin Kashmir.
-
Lebnon: Isra’ila Ta Kai Hari Kan Wata Mota Mutun Daya Yayi Shahada
Mamaya na ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar Lebanon daga lokaci zuwa lokaci ta hanyar kai hare-hare tare da kashe 'yan kasar ba tare da hukuma ta dauki wani mataki ba.
-
Ansarullah: Isra'ila Ta Tsallake Jajayen Layi, Tabbas Ta Jira Martanin Yemen.
Mamba a ofishin siyasa na kungiyar Ansarullah ta Yaman a martanin da yake mayarwa kan hare-haren da gwamnatin sahyoniyawa ta ke kai wa wannan kasa a yau ya ce: Sahayoniyawa sun tsallaka jajayen layi, kuma tabbas su jira martanin Yemen.
-
Isra'ila Ta Harba Bama-Bamai A Filin Jirgin Saman Sana'a + Bidiyo
Rundunar sojin Isra'ila ta ce filin tashi da saukar jiragen saman ya daina aiki gaba daya, inda suka zargi Houthis da amfani da shi wajen safarar makamai.
-
Maƙarƙashiyar Duniya "Mantawa Da Palastinu" Tare Da Haɗin Bakin Sarakunan Larabawa
Hujjatul Islam Jawad Naqwi ya karkare da cewa: Mantawa da Palastinu laifi ne; yin watsi da raunukan Gaza laifi ne; kau da kai daga kofofi da katangar masallacin Al-Aqsa laifi ne. Kuma idan wani talaka farar hula ne ya aikata wannan laifi, za a iya gafarta masa; Amma idan ya fito daga malamin addini, mai mulki, mai yada labarai, mai tunani, malamin jami'a, jami'in gwamnati, ko dan siyasa, wannan cin amana ba zai yuwu a gafarta shi ba.
-
Fursunonin Gidan Yarin Hillah Na Lardin Babil Sun Tsere, Ana Ci Gaba Da Bincike A Kansu
Iraki ta bayar da sanarwar tserewar fursunoni daga gidan yarin Hillah na lardin Babil, tare nemansu ruwa a jallo
-
Dakarun Yaman Sun Sanar Da Fara Hana Jiragen Isra'ila Ta Shi A Ko Ina
Sojojin Yaman sun fitar da wata sanarwa inda suka sanar da cewa za su kai hare-hare akai-akai kan filayen saukar jiragen sama na Isra'ila tare da katangewa ta sama kan gwamnatin kasar da nufin tallafawa al'ummar Palastinu.
-
Labarai Cikin Hotona | Yadda Mazauna Tulkarm Su Kai Gudun Hijira Biyo Bayan Gargadin Sojojin Sahayoniya
Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: dakarun gwamnatin sahyoniyawan sun ci gaba da kai hare-hare kan birnin Tulkarm da sansanonin sa na tsawon watanni kusan uku a ci gaba da fafatawa a fili tare da kaddamar da hare-hare da gargadin ruguza gidajen Palastinawa. A cikin sa'o'i 24 da suka gabata 'yan mamaya na yahudawan sahyuniya sun ba da umarnin rusa gidaje da gine-gine 106 na Palasdinawa a sansanonin 'yan gudun hijira na Tulkarm da Nur Shams.
-
Kungiyoyin Gwagwarmayar Sun Yaba Da Jinjina Harin Yamen Ga Isra'ila
Kungiyar Hizbullah da kwamitin Falasɗinawa da Kungiyar Hamas sun yaba da harin makami mai linzami da sojojin Yaman suka kai kan filin jirgin saman Ben Gurion
-
Yamen Ta Kai Hari Ga Filin Jirgin Ben Gurion Na Isra'ila+ Bidiyo
Majiyoyi na yaren Hebrew sun ba da rahoton cewa an yi ta jin karar ƙararrawa a Tel Aviv, biyo bayan harin da Yamen ta kai kan filin jirgin Ben Gurion.
-
Yemen Takai Harin Makamai Mai Linzami A Yankunan Da Aka Mamaye /Lieberman: Ba Mu Da Tsaro
A yayin da majiyoyin yahudawan sahyuniya suka bayar da rahoton cewa, sojojin kasar Yemen sun sake harba makamai masu linzami tare da jin karar kararrawar gargadi a arewacin yankunan da aka mamaye, tsohon ministan yakin haramtacciyar kasar Isra'ila, ya yi kakkausar suka kan ayyukan majalisar ministocin gwamnatin kasar, inda ya yi la'akari da yanayin tsaro a matsayin wani bala'i.
-
Bom Ya Tashi A Damascus / Tel Aviv Ta Kai Hari A Fadar Shugaban Ƙasa
An kai harin na Isra'ila a nisan mita 400 daga fadar shugaban kasa da ke Damascus.
-
Araghchi: Za A Gudanar Tattaunawa Zagaye Na Gaba A Roma
Ministan harkokin wajen Iran ya sanar da cewa, za a gudanar da zagaye na gaba na tattaunawa ba ta kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka dangane da shirin nukiliyar Iran da kuma dage takunkumin da aka kakaba mata a birnin Rome.
-
Hotuna | Yadda Gobara Ta Tashi A Yankunan Da Isra'ila Ta Mamaye
Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: wata gobara na ci gaba da bazuwa a tsaunukan birnin Kudus da aka mamaye, kuma an kwashe wasu mazauna yahudawan sahyoniya da ke cikin wadannan yankuna da aka mamaye sakamakon bazuwar wutar.
-
Hotuna: Yara A Khan Yunis Sun Buƙaci Kawo Ƙarshen Hare-Haren Ta'addancin Isra'ila
Kamfanin dillancin labaran AhlulBaiti: Yara a birnin Khan Yunus da ke kudancin zirin Gaza sun yi kira da a kawo karshen laifukan ta'addancin gwamnatin sahyoniyawa a wani gangami mai taken "Dakatar da yaki da kisan kare dangi da zalunci". Yara da suke dauke da tutoci masu taken "Badon Mutuwa Ba, Bafon Yunwa Ba". yaran sun yi jawabi ga al'ummomin duniya: "Muna mutuwa saboda tashin bamabamai, cututtuka, yunwa da kishirwa, kuma duniya ta yi shiru".
-
Hizbullah: Abin Da Ya Kamata A Sa A Gaba Shi Ne Janyewar Isra'ila Daga Lebanon
A cikin sabon jawabin nasa, shugaban kasar Labanon Joseph Aoun ya ce, takaita makamai ga gwamnatin kasar, wani mataki ne da aka riga aka dauka.
-
Amurka Ta Harba Bama-Bamai A Gidan Yarin Saada Da Ke Arewacin Yemen
A safiyar yau, hare-haren wuce gona da iri na sojojin Amurka da na 'yan ta'adda a kan wuraren zama a Yemen Mutane da dama ne suka mutu tare da jikkata sakamakon harin bam da aka kai a wani gidan yari da ke Saada.
-
Hotuna: Daren Farko Na "Taron Kasa Da Kasa Na Malaman Shi'a Karo Na Hudu" A Karbala.
Kamfanin dillancin labaran Ahlulbaiti (AS): An gudanar da taron kasa da kasa karo na hudu na fitattun malaman Shi'a a ranar Juma'a a kusa da haramin Imam Husaini (AS) a birnin Karbala.
-
Yamen Ta Sake Kai Hari Sansanin Navatim Na Isra'ila
Kasar Yemen ta sake kai wani hari da makami mai linzami kan sansanin 'Navatim' na gwamnatin Isra'ila
-
Hamas Ta Tattauna Da Masu Shiga Tsakani A Birnin Alkahira Kan Batun Tsagaita Wuta
Taron ya kuma jaddada bukatar daukar matakin gaggawa na kai agaji da kayayyaki ga al'ummar yankin.
-
Mummunan Darasi Ga Mamaya A Kwanton Baunan Shuja'iyya...Kasa Domin Yin Gwagwarmaya, Mutuwa Ga Mahara.
A farkon wannan arangama, ‘yan gwagwarmaya sun jefa makami mai linzami kan wata mota kirar Hummer ta sojoji da ta zo domin kwashe masu raunin, wanda alokacin aka jikkata wani soja. Sai kuma kashi na biyu na arangamar; Dakarun ‘yan gwagwarmaya suka kai hari kan tankar Isra'ila da makami mai linzami guda biyu, a cewar tashoshin Isra'ila.
-
Rahoto Kan Hare-Haren Da Gwamnatin Mamaya Ta Kai A Yankuna Daban-Daban Na Gaza Cikin Sa'o'i Kadan Da Suka Gabata
Dakarun mamaya sun kai hari a yankunan arewacin birnin Gaza, kuma a lokacin da aka kai hare-hare ta sama a yankin Al-Tuffah da ke gabashin birnin Gaza, Falasdinawa biyu sun yi shahada tare da jikkata wasu da dama.
-
Dubban 'Yan Ƙasar Yemen Ne Suka Gudanar Da Zanga-Zanga A Faɗin Ƙasar Domin Yin Allah Wadai Da Ta'addancin Amurka Da Isra'ila
Al'ummar kasar Yemen sun sake gudanar da jerin gwano a fadin kasar, inda suke jaddada goyon bayansu ga Falasdinawa yayin da suke yin Allah wadai da hare-haren da Amurka ke kaiwa kasarsu.
-
Araghchi Ya Isa Birnin Muscat Domin Shiga Tattaunawar Ba Ta Tsaye Ba Tsakanin Iran Da Amurka.
Ministan harkokin wajen Iran ya isa birnin Muscat ne domin halartar zagaye na uku na tattaunawar da ba ta kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, wanda masarautar Oman ke shiga tsakani.
-
Adadin Shahidai A Zirin Gaza Ya Karu Zuwa 51,439.
Rundunar Qassam: Mun bindige sojojin mamaya 4 da suka hada da sojoji biyu a gabashin Beit Hanoun da ke arewacin zirin Gaza.
-
Rahoto Cikin Hotuna Na Zaman Makokin Shahidar Imam Sadik (As) A Haramin Sayyidah Ma'asumah (As).
Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya kawo rahotan cewa: an gudanar da zaman makoki na ranar shahadar Imam Jafar Sadik (AS) tare da jawabin HUjjatul Islam "Sayyid HUssain Momini" da waken jaje daga Sayyid Ali HUssaininajad a cikin hubbaren Imam Khumaini (RA) Shabestan na Haramin Sayyidah Ma'asumah (As).
-
Ansarullah: Wajibi Ne Ga Al'ummar Musulmi Su Tanadi Ƙarfin Kare Kansu
Jagoran Ansarullah na kasar Yaman: Makiya yahudawan sahyoniya a Gaza ba su iya katabus na soji ba, don haka suka koma yin karya.
-
Juyayin Shahadar Imam Ja'afar Sadik (AS)
Al'ummar Musulmai mabiya mazhabar Shi'a a faɗin duniya sun gudanar da zaman makokin shahadar Imam Sadik (a) shugaban mazhabar shia Imamiya a daren jiya da yau.