Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Mujahidan Yamen sun rubuta a dandalin "X", su na gargadi ga girman kai na duniya da Amurka ta wakilta: Duniya ba za ta manta cewa Mujahidan Yamen sun yi abin da ya tilasta wa Trump tattare jiragen ruwansa daga gabar tekun Yemen ya mai da su gida.
Lokacin da Mujahidan Yamen suka ce "nan ba da daɗewa ba," ba wai kawai taken haka kawai ba ne a yanar gizo, sai dai yakamata a fahimci gaskiyar lamarin bias gogewa.
Wannan itace Yemen ɗin da ta canza daidaiton iko a cikin Tekun Ahmar, ta girgiza tattalin arzikin duniya, kuma ta durkufar da hanyoyin jigilar jiragen ruwa na Yamma da ikonta.
Mujahidan Yamen wanda sun tabbatar da cewa idan haƙƙin kare fagen tsakiya ne, to nisan ƙasa ba shi da mahimmanci.
Saƙon wannan bidiyon da wannan taƙaitaccen bayani na dabarun shine idan maƙiya su na tunanin Iran ita kaɗai ce, to hakan kuskure ne tsantsa.
Matsayin gwagwarmaya shine hanyar sadarwa mai rai, kuma idan wani ɓangaren ta ya lalace, sauran za su motsa.
Wannan shine mafarkin da Washington da Tel Aviv ke tsoro.
Your Comment