Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Majiyoyin labarai sun ruwaito cewa wani jirgin saman Isra'ila mara matuki ya kai hari a wani yanki a gabashin Lebanon.
An kai harin ne a garin Duras, kusa da Asibitin Daral-Amal a yankin Bekaa a gabashin Lebanon.
Har yanzu babu wani rahoto kan yanayin abin da aka nufata da kuma asarar rayuka ko barnar da harin jirgin saman mara matuki ya yi.
Your Comment