20 Janairu 2026 - 23:30
Source: ABNA24
Isra'ila: Rundunar Ƙasa Da Ƙasa Ba Za Ta Shiga Gaza Ba Idan Har Hamas Ba Ta Ajiye Makamai Ba

Isra'ila ta yi ikirarin cewa duk wani yunƙuri na ƙirƙirar irin wannan rundunar yayin da Hamas ke da makamai kuma tana iko da yankunan yamma da "Layin Rawaya" zai zamo kawai a banza ba tare da ikon zartarwa ba.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Wannan kimantawa tana da alaƙa da yanayin siyasa bayan ganawar da aka yi tsakanin Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da Shugaban Amurka a Florida makonni biyu da suka gabata. Majiyoyin Isra'ila sun ce Netanyahu ya sami ƙarin 'yancin yin aiki a Gaza bayan goyon bayan Trump kwanan nan.

A cewar majiyoyin, Majalisar Zaman Lafiya da gwamnati a Gaza za su aiwatar da mataki na biyu na shirin shugaban Amurka ne kawai idan aka samar da wata hanya don kwance damarar yaƙi da Hamas da kuma kawar da kwace dukkan makamai a Gaza.

Majiyoyin sun yi iƙirarin cewa bayan kafa majalisar zaman lafiya da gwamnati, za a bai wa Hamas kimanin watanni biyu don ajiye makamanta. 

Duk da haka, koma me aka tsara ita Hamas ba za ta amince ta ajiye makamanta ba, gami da ƙananan makamai.

Your Comment

You are replying to: .
captcha