7 Faburairu 2026 - 21:42
Source: ABNA24
Isra’ila Ta Mika Akwatunan Gawarwakin Shahidai 66 Da Kawai Kokunan Kawukansu Ne A Ciki

Mohammed Abu Salmiya, darektan Al-Shifa Medical Complex da ke Gaza, ya bayyana cewa kiyasi ya nuna cewa har yanzu akwai kimanin mutane 10,000 da har yanzu ba tono su ba a ƙarƙashin tarkacen da ke Zirin Gaza. Kuma makomar wasu kimanin 5,000 ba a san yadda ta ke ba.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Mohammed Abu Salmiya, darektan Al-Shifa Medical Complex da ke Gaza, ya bayyana cewa kiyasi ya nuna cewa har yanzu akwai kimanin mutane 10,000 da har yanzu ba a tono so ba a ƙarƙashin buraguzan gina ginen da Isra’ila ta rusa a Zirin Gaza. Kuma har yanzu ba a san makomar wasu kimanin 5,000 ba.

Abu Salmiya ya ce sojojin mamaya sun miƙa akwatunan gawawwaki 66, wanda kawai suna ɗauke ne kawai da ƙoƙunan kwakwalan shahidai. Ya kuma ambaci cewa an miƙa gawawwakin mata da dama ba tare da wani bayani game da inda aka ɗauke su ba.

Daraktan Cibiyar Kiwon Lafiya ta Al-Shifa ya tabbatar da cewa an yanke wasu gabban gawarwakin, kuma a wasu lokutan, an zaga cikinsu sannan aka dinke su. Ya kara da cewa akwai shaidar cewa an ɗebe wasu kayayyaki daga cikin gawarwakin daga wasu fursunonin da suka mutu a Gaza.

Abu Salmiya ya ci gaba da cewa hukumomin mamaye sun san asalin gawarwakin da suka bayar, amma sun ki bayar da wani bayani game da lamarin.

Your Comment

You are replying to: .
captcha