27 Janairu 2026 - 09:26
Source: ABNA24
Masu Sa Ido Na Turai Da Ma'aikatan Falasdinawa Sun Hallara Don Sake Buɗe Mashigar Rafah

Jaridar Yedioth Aharonot ta ruwaito cewa masu sa ido na Turai da ma'aikatan Falasdinawa sun hallara a mashigar Rafah a halin yanzu don shirya sake buɗe mashigar kan iyakar.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Shirye-shiryen da aka amince da su sun haɗa da ba wa gwamnatin Isra’ila jerin sunayen waɗanda zasu ketare mashigar ta Rafah kowace rana, wanda hukumar tsaro ta gwamnatin (Shabak) ta yi rijistarsu kuma ta tabbatar.

Yedioth Aharonot ta ruwaito cewa masu sa ido na Turai sun ɗauki watanni suna horo don gudanar da sake buɗe hanyar Rafah kuma yanzu sun shirya don aiwatar da wannan aikin nan take.

An yi tsammanin sake buɗe hanyar a ƙarƙashin matakin farko na yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, amma gwamnatin Isra’ila ta hana sake buɗe ta har zuwa yau, tana mai karya alkawuranta.

Your Comment

You are replying to: .
captcha