28 Janairu 2026 - 10:34
Source: ABNA24
Isra’ila Ta Tone Kaburburan Falasdinawa 200 Don Neman Gawar Wani Sojan Isra'ila.

Isra’ila ba ta takaita da gamsuwa da kai hari kan masu rai ba a yankin Gaza sai dai ma Isra'ila ta fadada zaluncinta ga waɗanda aka binne tun da daɗewa a unguwar Al-Tuffah da ke gabashin birnin Gaza. Ta tone makabartar Al-Batsh, inda ta tone kaburburan a wani wuri mai ban tausayi da tayar da hankali, kamar dai matattu da kansu sun zama shaidu ga wannnan yaƙin na rashin Imani da tausayi.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Aikin na kwanaki biyu ya ƙunshi haƙo gawarwakin Falasɗinawa da kuma yin rushe ɗaruruwan kaburbura. In da ta tona gawarwakin Falasɗinawa guda da aikewa da su Cibiyar Binciken ta Abu Kabir don a yi musu bincike don tantance asalin sojan Isra'ila, Ran Goili.

Wani mummunan tashin hankali na jin kai da ɗabi'a a bayyane ya ke kamar yadda masu fafutuka suka nuna: Isra'ila ta tattara sojojinta don tono kaburbura don neman gawa ɗaya, yayin da sama da shahidai 10,000 na Falasɗinawa suka kasance a ƙarƙashin tarkacen da ke Zirin Gaza, duniya ba ta kula da makomarsu ba.

Al’ummu Sun Nuna Fushin Su Akan Wannan Lamari.

Wani hoton sama da ke nuna ayyukan bincike a makabartar Al-Batsh ya haifar da fushi a shafukan sada zumunta. Hoton ya nuna girman lalata kaburbura da kuma bayyanar gawawwaki, ba tare da nuna damuwa ga mutuncin ɗan adam ba, duk da haka an yi shine wai don neman sojan Isra'ila.

Masu amfani da Twitter sun ishara da cewa hare-haren da aka kai a Gaza ba su takaita ga rayuwar masu rai ba - kashe-kashe, korar ma'aikata, da lalata gidaje da kadarori – har ma ta kai ga matattu da kansu, tare da tono kaburbura sama da 200 na shahidai da mazauna yankin.

Masu fafutuka sun bayyana cewa harin bai takaita ga masu rai ba, kuma babu wani lura ko wani la'akari na jin kai ko na addini. Wadanda aka kasha suma ba su tsira daga zaluncin da ake yi wa mutane ba, kuma ba a girmama matattu a cikin kaburburansu ba. Gaskiyar da ke ƙasa ana aiwatar da ita ba tare da tausayi ba, ko wanda aka kashe yana da rai ko ya mutu.

Wannan keta hakki da ɗabi'a da ɗan adam. Masu fafutuka sun bayyana abin da ke faruwa a makabarta—hako gawawwaki sama da 200 daga cikin kaburbura 450 don duba ko gawar soja Ghweili tana cikinsu—a matsayin laifi ga ɗan adam da ɗabi'a. Sun nuna cewa bayan binciken, ana jefa gawawwakin kamar jakunkunan shara a kan shinge tare da binne su a cikin kaburburan bai daya ba tare da mutunci ba.

Sun ƙara da cewa wannan keta hakki a fili ga dukkan ɗabi'un ɗan adam, domin an tona tare da jefa gawawwakin a rami daya da binne su ba tare da girmama mutunci ba.

Wasu sun yi ishara da cewa kai hari ga makabartu abu ne mai wuya a tarihin soja, wanda ke haifar da tambayoyi masu zafi game da ɗan adamtaka na waɗannan ayyuka. Sun jaddada cewa akwai alhakin ɗabi'a, kuma mutuncin ɗan adam ba ya ƙarewa ko da bayan mutuwa.

Wani mai fafutuka ya rubuta cikin fushi: "Don kare gawar wani soja na Isra'ila, an rufe hanyar shiga ta Rafah, kuma an hana wadanda aka jiwa rauni da wadanda suka ji rauni samun magani a kasashen waje. A yau, mamayar tana tono kaburburan shahidai sama da 200 na Falasdinawa, tana lalata tsarkin mutuwa da kuma lalata kaburburan shahidai, duk don neman gawar wani fursuna na Isra'ila. An lalata mizanin adalci, rashin adalci ya bayyana, amma gaskiya ta fi dukkan labaransu haske".

Wani dan kasa ya shaida ta dandalin "X", yana nuna girman bala'in: "A cikin makabartar da aka binne matata da 'ya'yana, suna neman gawar soja na karshe tun jiya. Sun kashe su kuma sun jefa bam a gidan da ke kansu, kuma a yau suna lalata makabartarmu da kaburburansu. Bayan yau, ba za mu sami kaburbura da suka rage ba bayan sun lalata ta".

Masu rubutun ra'ayoyi a yanar gizo sun yi tambaya game da ƙiyayyar da ta sanya mamaya ta bi matattun a cikin kaburburansu bayan sun kasa gamsuwa da kisa da kewanya ga Falasdinawa, suna masu jaddada cewa dole ne a girmama mutuncin Falasdinawa ko da bayan mutuwa.

Masu fafutuka sun kammala da cewa duniya tana yin watsi da wahalar da Falasdinawa sama da miliyan biyu da Isra'ila ta yi garkuwa da su a cikin mawuyacin hali, baya ga wasu Falasdinawa kimanin 9,000 da aka sace a cibiyoyin azabtarwa ta Isra'ila da kuma dubban gawarwakin Falasdinawa waɗanda ba a san makomarsu ba.

Your Comment

You are replying to: .
captcha