22 Janairu 2026 - 21:27
Source: ABNA24
Falasdinawa 11 Sun Yi Shahada A Hare-Haren Isra'ila 

Wata kafar yada labarai ta Falasdinu, tana yi nuni da harin da aka kai a Gaza wanda yayi sanadiyar shahadar Palastinawa 11 da suka hada da 'yan jarida da dama.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Jaridar ta bayyana wannan wani karya Yarjejeniyar tsagaita wuta ne daga ɓangaren Isra'ila tun daga ranar farko Isra'ila ba tai kasa agwiwa ba wajen kai hare-haren da kin hin duk wani mataki da wannan yarjejeniya ta kunsa na mutumtaka da siyasa, duk da ikirarinta game da kashi na biyu da kokarin aiwatar da mataki na biyu wanda gwamnatocin ƙasa da ƙasa ke shiga tsakani. 

A rana ta 111 da yarjejeniyar tsagaita wuta a zirin Gaza, Falasdinawa 11 sun yi shahada sakamakon luguden wuta da harsasai na Isra'ila, ciki har da 'yan jarida uku da suke ba da rahotannin halin da sansanonin 'yan gudun hijira ke ciki a tsakiyar Zirin Gaza, wasu da dama sun samu raunuka daban-daban. 

Wadannan abubuwan da suka faru sun nuna cewa keta yarjejeniyar da Isra'ila ta ke ci gaba da yi ya ci gaba daga ranar farko ta yarjejeniyar da ba ta dawwama ba. 

Wadannan hare-haren suna faru ne a daidai lokacin da zirin Gaza ke ci gaba da fama da mummunan yanayin jin kai kuma har yanzu ana rufe da hanyoyin kuma ana sarrafa shigar da agaji da man fetur, ba tare da samar da wani ci gaba na azo a gani a rayuwar mazauna ba.

Your Comment

You are replying to: .
captcha