21 Janairu 2026 - 19:16
Source: ABNA24
Isra'ila Ta Kai Hari Ga Kwamitin Masar Da Ke Kula Da Tsagaita Wuta A Zirin Gaza

Majiyoyin Falasdinu sun ruwaito cewa gwamnatin Sahiyoniya ta kai hari kan wata mota da ke dauke da membobin kwamitin Masar da ke kula da tsagaita wuta a Zirin Gaza.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Masar ta nemi Isra'ila da ta bayar da bayani game da dalilan da suka sa aka kai hari ga mambobin kwamitin Masar a Zirin Gaza.

Kungiyar Jihadin Musulunci ta Falasdinu tace: Harin da aka kai wa kwamitin Masar ya kunshi sakon siyasa cewa gwamnatin Sahyoniya na adawa da mataki na biyu na tsagaita wuta.

Your Comment

You are replying to: .
captcha