3 Faburairu 2026 - 13:04
Source: ABNA24
Jirgin Ruwan Amurka Abraham Lincoln Ya Ja Da Baya Da Nisan Kilomita 1,400 Daga Tashar Jiragen Ruwa Ta Chabahar

Rundunar Jiragen Ruwa ta Amurka ta USS Abraham Lincoln, tare da wasu jiragen ruwa na karkashin ruwa, a halin yanzu tana nan kusa da Tekun Aden da kuma gabashin Tsibirin Socotra a kudancin Yemen.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Wata majiya mai tushe a fannin leken asiri ta soja ta ruwaito cewa Jirgin Ruwan Amurka Abraham Lincoln, tare da wasu jiragen ruwa masu na karkashin ruwa, suna nan a kusa da Tekun Aden da kuma gabashin Tsibirin Socotra a kudancin Yemen.

A cewar majiyar, jiragen ruwan suna da nisan kilomita 1,400 daga Tashar Jiragen Ruwa ta Chabahar a kudu maso gabashin Iran.

A cikin 'yan kwanakin nan, Iran ta yi barazanar cewa hare-haren Amurka za su jefa Yammacin Asiya ga mummunan hadarin yakin yanki da kuma duniya ga farashin mai sama da dala $150.

Manjo Janar Mousavi, Babban Hafsan Hafsoshin Soja, shi ma ya sanar a hukumance jiya cewa akidar sojojin Iran ta canja daga kariya zuwa kai farmaki.

Your Comment

You are replying to: .
captcha