Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Harin ya yi sanadiyyar shahadar 'yan jarida uku da kuma raunata wasu da dama, wadanda aka ruwaito cewa wasu daga cikinsu suna cikin mawuyacin hali.
A cewar wadannan rahotanni, 'yan jaridar da aka kai hari suna gudanar da wani aikin jarida tare da daukar hoton wani sansani da ke da alaƙa da "Kwamitin Masar" a yankin; Kwamitin Masar Wata kungiya ce da ta dade tana aiki a cikin 'yan watannin nan a fannin samar da agaji da kuma samarwar da 'yan gudun hijirar yaki a Gaza wuraren fakewa.
Shaidu sun jaddada cewa motar da aka kai hari ta kasance ta fararen hula da kafofin watsa labarai kuma ba a ga wani aikin soja a wurin ba.

A cewar shaidar gani da ido, an kai gawarwakin shahidai da wadanda suka jikkata zuwa cibiyoyin lafiya kuma kungiyoyin agaji suna fuskantar karancin kayan aikin likitanci.
Your Comment