Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa "mika gungun ‘yan ta’addan ga hukumomin Iraki da Amurkawa suka yi an gudanar da shi ne a hukumce, kuma ya kunshi wasu ‘yan kasashen Turai, Asiya, da Larabawa".
Sun kara da cewa "za a rarraba fursunonin ISIS a tsakanin Gidan Yarin Susa da ke Sulaymaniyah, Gidan Yarin Al-Hout da ke Nasiriyah, da Gidan Yarin Cropper kusa da Filin Jirgin Sama na Baghdad".
An ambaci cewa "hukumomin Iraki sun ware jagorori masu hadari na shugabannin ISIS daga wasu membobi, da wasu mutanen da ba su da hatsari".
Gwamnatin Iraki ta tabbatar da cewa yunkurin mayar da 'yan ta'addan ISIS daga yankin Siriya zuwa Iraki mataki ne na kariya da nufin kare tsaron kasar Iraki. Ta bayyana cewa ba a yanke wannan qudir ba bisa ka'ida ba sai dai an yi shi ne bisa nazari da tantancewa sosai, kuma an riga an fara shari'ar wadannan mutane.
........
Your Comment