Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya kawo wani bangare na huxubar da limamin Juma'a na birnin Alishashr dake Lardin Bushahr a Iran Hujjatul-Islam Walmuslimeen Muhammad Hamidinejad Imam na Alishahr Juma'a inda ya ce Acikin huduabrsa daya gabatar a wannan juma'ar data gabata cewa: Wannan rana Ita ce ranar Maulidin Sayyida Fatima Ma'asumah A's. Dangane da girman wannan baiwar Allah a wacce misalta cikakkiyar mace a Musulunci, ina so in ambaci wata ruwaya daga Imam Sadik A's, Wanda aka samu ruwayar hakan shekaru kafin a haifi wannan Sayyidah riwayar tana cewa: Allah yana da hubbare wanda yake shi ne Makkah, kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wa'alihi Wasallama yana da hubbare wanda yake shi ne Madina Imam Ali A's Yana da Hubbare wanda ya ke shi ne Kufah, kuma muma AhluBayt muna da Hubbare wanda ya ke shi ne Kum, kuma nan gaba za a binne 'ya daga cikin 'ya'yana ana ce da ita Fatima a can, duk wanda ya ziyarce ta zai shiga Aljanna.
A fili yake ma'anar haramin ba wai kawai binne mutum ba ne, a'a wuri ne, domin ba za a iya cewa hakan ga Allah ba, kuma babu daya daga cikin limamai da aka binne a Kum, sai dai hubbare shi ne wurin da mazhabar mutum da akidar mutum suke rayuwa kuma da jama'ar wurin suke raya koyarwa da Mazhaba ta Ahlul-baiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, kuma wajen da mazhabar shi'anci take rayuwa, misali daya daga cikin wadannan da suka yi karatu a Wajen shine Shaikh Zakzaky, wanda ya Shi'antar da miliyoyin mutane a Najeriya.
Kuma ranar haihuwarta yau kenan ana kiranta da ranar 'ya mace, wani abu daya shine Allah madaukakin sarki ya fitar da sharudda na tantance 'ya Mace mai kamala wacce ta cancanta. Kuma shaidan ya bayyana nasa sharudda ga 'ya Mace anasa ganin a duk shekara ana gudanar da babban taro na zabar 'Ya Mace data fi cancanta a duniya, kuma mata da 'yan mata daga ko'ina cikin duniya suna shiga cikin wannan taro, wanda a ganin kasashen waje wanda sune shaidan a yau sun dauki cancanta shine kyawun waje na zahiri kawai na mace a matsayin shine kamala wanda ya zamo duk wacce tafi kyawun fuska to ita za'a zaba a matsayin wacce tafi cancanta. Amma kuma Allah ya tanadar da ma'aunai na cancantar kamala ga 'Ya Mace a cikin Alkur'ani mai girma, cewa duk yarinyar da take son a gabatar da ita kuma Allah ya zabe ta a matsayin mace ta dace tafi cancanta, to tayi koyi da da wadannan ma'aunan, a cikin aya ta 35 ta surar Ahzab Allah Ta'ala ya ce: Yarinya mace ta zamo Musulma kuma Mumina a wajen Allah Ta kasance mai kaskantar da kai, mai gaskiya da hakuri a cikin wahala, ta rika taimakon mabukata, ta rika yin azumi da gujewa cudanya da wadanda ba Muharramanta ba, kuma ta kasance mai yawan ambaton Allah, wannan ita ce sifar 'Ya Mace mai cancanta. Acikin aya ta 25 surar Qasas Allah Ta'ala ya girmama tare da jinjinawa 'ya mace da ta ke tafiya acikin kunya da natsuwa. A cikin Surar Tahreem Allah Ta'ala yana jinjina ga 'Ya Mace mai kame kanta da kiyaye tsiraicinta. A cikin aya ta 31 surar Nuur ya girmama da yabo ga 'ya mata masu gujewa nunawa tsiraici da ado, 'yammata salihai ba masu sakin gashin kansu ya fito waje kuma ba sa gabatar da kansu ga wadanda ba mazajen aurensu ba ne, Ma'aunai agun Allah su ne kunya da tsafta da kuma rashin nuna tsiraici da ado a wajen da ya haramta. Yanzu dai zaɓin ya rage ga ’ya'ya mata shin suna so a zaɓe su a matsayin ƴan matan da suka fi bangaren Shaiɗan ko a zaɓe su a bangaren Allah a matsayin wadanda suka fi.
Mu yi amfani da watan Zul-Qaida yadda ya kamata, Watan ne da ya fara da Haihuwar Sayyidah Ma'asumah (A.S) kuma ya kare da Haihuwar Imam Rida (A.S) a kwanaki goma na farko.
Wanda Imam Ali A's ya ce idan kana so ka samu mutumci to ka zama mai takawa, in ka aikata zunubi zaka fita daga cikin karamci, sai ya zama makaskanci kuma tsinan ne.




