Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

4 Faburairu 2024

11:19:59
1435063

Iran Na Daga Cikin Kasashe 10 Na Gaba A Fannin Fasahar Zirga-Zirgar Jiragen Sama

Ayatullah Raisi ya jaddada cewa, nasarorin da aka samu ta hanyar kokarin matasa, kwararru da dakarun kasar Iran, a hakikanin gaskiya ma'auni ne na taken "Zamu Iya".

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (AS) – ABNA- ya habarta cewa: Shugaban kasar Iran Sayyid Ebrahim Raisi ya bayyana cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana cikin kasashe 10 na gaba a fannin fasahar jiragen sama a duniya.

Da yake magana jiya Asabar a birnin Tehran a yayin bikin ranar fasahar sararin samaniya ta kasa, shugaban na Iran ya bayyana cewa, duk da cewa makiya sun yi kokarin dakile tare da killace al'ummar Iran ta hanyar sanya takunkumi, nasarar harba tauraron dan adam 11 ya kawo cikas ga dukkan takunkumin hana RAN da aka sanya mata shirin mayar da kasar Iran saniyar ware.

Ayatullah Raisi ya jaddada cewa, nasarorin da aka samu ta hanyar kokarin matasa, kwararru da dakarun kasar Iran, a hakikanin gaskiya ma'auni ne na taken "Zamu Iya".

Babban shugaban na Iran ya ci gaba da cewa, makiya ta hanyar kafafen yada labarai suna kokarin sanya yanke kauna a cikin al'ummar Iran, sai dai ya kara da cewa malaman Jamhuriyar Musulunci ta Iran suna bullo da sabbin abubuwa da dabaru da kirkire-kirkire wadanda a kansu manyan ayyuka ne da suka cancanci a yaba masu.

Ya zuwa karshen shekarar Iran da ake ciki, wanda zai kare a ranar 21 ga Maris, yawan tauraron dan adam da ake kafawa a sararinn samaniya zai kai 30.