Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

23 Satumba 2023

04:32:47
1395177

Haramtacciyar Kasar Israila Ta Bayar Da Gawar Shahid "Bilal Qadh" Daga Ramallah

Hukumar kula da fararen hula ta Falasdinu a cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin jiya Juma'a, ta ce sojojin Isra'ila sun yanke shawarar mika gawar shahidi Bilal Ibrahim Qadh (mai shekaru 33)...

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, an gano gawar shahidi Bilal Qadh a kauyen Shaqiya da ke yammacin Ramallah a tsakiyar gabar yammacin kogin Jordan.

A cikin wata sanarwa da hukumar kula da harkokin jama'a ta Palasdinu ta fitar a yammacin jiya Juma'a ta fitar da ke cewa sojojin Isra'ila sun yanke shawarar mika gawar shahidi Bilal Ibrahim Qadh (mai shekaru 33) daga kauyen Shaqiya da ke yammacin Ramallah a yau."

Qadh ya yi shahada ne a ranar 10 ga watan Yuli, bayan da sojojin mamaya sun bude masa wuta a wani guri da ke kusa da kauyen "Deir Nizam" da ke yammacin Ramallah, inda suka ce ya jefa musu wani gurneti ne.

Shahidi Bilal Qadh, mutum ne mai ‘ya’ya uku, maza biyu da ‘ya mace, babban cikinsu dan shekara goma ne.

Dakarun mamaya na Isra'ila sun rike gawawwakin shahidai 256 a cikin kaburburan da ake kira lamba, baya ga 142 a cikin mutuware, a cewar alkaluman da kwamitin gaggawa na kungiyar 'yan fursuna ta kasa ya fitar a karshen watan Agusta.

.........................