Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

14 Mayu 2023

16:54:56
1365649

Hare-haren Ta'addanci A Najeriya Ya Haifar Da Matsalar Karancin Abinci

Hare-haren Boko Haram da kungiyar ISIS reshen Najeriya ya sanya Najeriya na fuskantar matsalar karancin abinci ga mazauna yankunan arewa maso gabashin kasar.



Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Al'ummar jihohin Adamawa, Borno da Yobe da ke Najeriya an tilasta masu barin yankin sakamakon hare-haren da sojojin kasar suka yi na yakar kungiyoyin 'yan ta'adda na Boko Haram Najeriya reshen kungiyar ISIS (ISWAP) da karuwar tashe-tashen hankula, sun haifar da wuraren da ba su da tsaro da karancin abinci da matsalolin gidaje.


Manya da hare-haren ta'addanci ya raba da muhallansu da matsuguni a sansanoni suna fama da yunwa, kuma yara na fama da rashin abinci mai gina jiki.


Manoman sun daina aiki tare da barin gonakinsu saboda yawaitar hare-haren ta'addancin Boko Haram da kungiyar ISIS reshen Najeriya.


A daya bangare kuma, ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya ya yi gargadin cewa mutane miliyan 4.3 a arewa maso gabashin kasar na fuskantar matsalar karancin abinci kuma lamarin zai kara tabarbarewa idan ba a dauki matakan gaggawa ba.


Gabriele Santi, kodinetan kungiyar likitocin da ba sa iyakoki a jihar Borno, ya shaida wa Anatoly cewa, matsalar karancin abinci mai gina jiki da aka yi rajista tun farkon wannan shekarar ta kai matsayi mafi girma idan aka kwatanta da na bara.


Ya kara da cewa: Yawan karuwar yaran da ke fama da rashin abinci mai gina jiki na bukatar hanzarta fadada ayyukan rigakafi da magani don hana kai wa ga bala'in yunwa.


Idan dai ba a manta ba, a shekarar 2000 ne kungiyar Boko Haram ta sanar da wanzuwarta, kuma tun daga shekarar 2009 zuwa yanzu akalla mutane 2000 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-hare da ta’addancin wannan kungiya.


Tun a shekarar 2015 ne wannan kungiyar ta'addanci ta fara kai hare-haren ta'addanci a kasashen Kamaru, Benin, Chadi, Nijar da Najeriya. Dubban daruruwan mutane ne aka tilastawa yin hijira a Najeriya saboda tashe-tashen hankula da hare-haren ta'addanci a kasar.


.........................