Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

3 Oktoba 2022

17:52:29
1310168

Rashin Kwanciyar Hankali Da Ke Faruwa Tsararran Shiri Ne Da Aka Tsara Shi

Cikakken Bayanan Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Dangane Da Abubuwan Da Suke Wakana A ‘Yan Kwanakin Nan A Iran

Babban kwamandan a wajen bikin yaye daliban jami’o’in hafsoshin sojan kasar hadin gwiwa, inda ya jaddada cewa, dangane da abubuwan da suke faruwa na a cikin kasa a yan kwanankin nan an shirya wannan tarzomar dake faruwa, ya ce: ko da ba batun yarinyar nan ba, to zasu fake da wani abun don haifar da rashin tsaro da tarzoma a kasar

Babban kwamandan a wajen bikin yaye daliban jami’o’in hafsoshin sojan kasar hadin gwiwa, inda ya jaddada cewa, dangane da abubuwan da suke faruwa na a cikin kasa a yan kwanankin nan an shirya wannan tarzomar dake faruwa, ya ce: ko da ba batun yarinyar nan ba, to zasu fake da wani abun don haifar da rashin tsaro da tarzoma a kasar a ranar farko ga watan Mehr na bana Ina fada a fili cewa wadannan tarzoma da rashin tsaro da Amurka da gwamnatin sahyoniyawan mamaya su suka tsara, kuma masu karbar albashinsu da wasu maciya amana Iraniyawa da ke kasashen waje ne suka taimaka musu.


Muhimman Batutuwa Da Ke Cikin Maganganun Jagoran Juyin Su Ne Kamar Haka;


* Mutuwar yarinyar itama ta sosa mana zukatanmu / daukar matakin da aka yi ba tare da bincike ba, ya haifar da tashin hankali da rashin tsaro ga jama'a tare da afkawa hurumin Al-Qur'ani, masallaci, hijabi, banki da motar talakawa ba kamar yadda aka saba ba, wanda duka an yi shirya shi ne.

* A cikin wadannan abubuwan da suka faru a cikin 'yan kwanakin nan, sama da komai an zalunce jami'an tsaron kasar, an zalunci Basij, an zalunci al'ummar Iran. Sun zalunce su sosai, Tabbas al'umma sun bayyana karfin hali a wannan lamari kamar yadda ya faru a sauran al'amuran, sun nuna cikakken karfi, kamar yadda aka saba, kamar yadda aka saba a baya, haka za ta kasance a nan gaba ma. A nan gaba, duk inda makiya suke son haifar da tarzoma, jajirtattun al'ummar Iran su ne ke kare kansu da tasiri. Suna masu shiga filin kuma sun shig a wannan ma.

* Na'am, al'ummar Iran an zalunce su, amma tana da karfi kamar Amirul Muminin, kamar ubangidanta Ali, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, wanda ya kasance mai karfi, mafi karfi, kuma shine mafi zalunta.

*Wannan lamarin da ya faru, na rasuwar wata yarinya. Hakane lamari ne mai daci. Zuciyarmu kuma ta yi zafi. Amma abin da ya faru a kan wannan lamari, ba tare da bincike ba, ba tare da wani tantantaccen abu ba, hakan yana nufin shikenan sai wasu su fito kan titi ba suyi hargitsa ba, su haifar da rashin tsaro ga jama’a, da hargitsa tsaro, da kona Alqur’ani, su cire hijabi daga kan mace mai lullubi, su kona masallacin da Husainiya, su kona bankin, sannan su banka wa motocin mutane wuta. Wannan martani ga lamarin wanda yazamo abin takaici, wannan baya wajabta haifar tare da aiwatar da irin waɗannan ayyukan, waɗannan ayyukan bana dabiance bane, ba na halitta bane. Wannan tashin hankali da hargitsi an shirya shi ne.


* A ra'ayi na, waɗansu fuskoki na (wasu wasanni da masu fasaha) ba su da mahimmanci kuma bai kamata su kasance an maida hankali wajen kula da su ba. Al'ummarmu masu fasaha da wasanni suna cikin koshin lafiya kuma akwai da yawansu masu aminci da daraja a ciki, kuma matsayin 'yan tsirarun mutane ba shi da daraja. Ya rage ga bangaren shari’a kan ko matsayinsu na laifi ne ko a’a, amma a dunkule matsayin wadannan mutane ba shi da wata kima, kuma al’ummar fasaha da wasanni ba za su gurbata da wadannan batutuwa na makiya ba.


Cikakkun Bayanai Na Kalaman Jagoran Juyin Sune Kamar Haka;


A safiyar yau (Litinin) ne babban kwamandan sojojin kasar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a wajen bikin yaye daliban jami'o'in hafsoshin sojan kasar, ya gabatar da muhimman jawabai, inda yake ishara da abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, ya kuma jaddada cewa: Ina fadin cewa wadannan abubuwan da suka faruwa shirin Amurka, gwamnatin sahyoniya da mabiyansu ne. Babban matsalarsu ita ce ta Iran mai karfi mai cin gashin kanta da kuma ci gaban kasar. Al'ummar Iran sun bayyana da karfinsu a cikin wadannan al'amura kuma za su kasance haka nan gaba, kuma zasu shiga cikin fage da jarumtaka a duk inda ya dace a nan gaba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci a farkon shiga dandalin ya halartar kabarin shahidan da ba a iya gane su ba, inda yayi masu adduah Fatiha ya jinjina wa jarumai da jarumtakarsu na kare Musulunci da Iran.

Daga nan sai babban kwamandan ya ga sassan da ke dandalin Sun.

A cikin wannan biki, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana a cikin muhimman kalmomi game da abubuwan da suka faru a kasar da cewa: A cikin wadannan abubuwan da suke faruwa an fi zaluntar jami'an tsaron kasar da Basij da al'ummar Iran fiye da komai. Tabbas al'ummar Iran sun bayyana kwarin gwiwa a cikin wannan lamari da ma wasu lamura, kuma a nan gaba ma haka za ta kasance.

Ayatullah Khamenei ya jaddada cewa: A nan gaba a duk inda makiya suke son haifar da tarzoma, jajirtattu kuma muminai na Iran za su fito domin kare kawunansu.


A cikin wannan lamari da ya faru, na rasuwar wata yarinya, wanda hakan ya karya mana zuciya

Na'am, al'ummar Iran an zalunce su, amma tana da karfi kamar Amirul Muminin, kamar ubangidanta Ali, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, wanda ya kasance mai karfi, mafi karfi, kuma shine mafi zalunta.

*Wannan lamarin da ya faru, na rasuwar wata yarinya. Hakane lamari ne mai daci. Zuciyarmu kuma ta yi zafi. Amma abin da ya faru a kan wannan lamari, ba tare da bincike ba, ba tare da wani tantantaccen abu ba, hakan yana nufin shikenan sai wasu su fito kan titi ba suyi hargitsa ba, su haifar da rashin tsaro ga jama’a, da hargitsa tsaro, da kona Alqur’ani, su cire hijabi daga kan mace mai lullubi, su kona masallacin da Husainiya, su kona bankin, sannan su banka wa motocin mutane wuta. Wannan martani ga lamarin wanda yazamo abin takaici, wannan baya wajabta haifar tare da aiwatar da irin waɗannan ayyukan, waɗannan ayyukan bana dabiance bane, ba na halitta bane.

inda ya jaddada cewa, dangane da abubuwan da suke faruwa na a cikin kasa a yan kwanankin nan an shirya wannan tarzomar dake faruwa, ya ce: ko da ba batun yarinyar nan ba, to zasu fake da wani abun don haifar da rashin tsaro da tarzoma a kasar a ranar farko ga watan Mehr na bana Ina fada a fili cewa wadannan tarzoma da rashin tsaro da Amurka da gwamnatin sahyoniyawan mamaya su suka tsara, kuma masu karbar albashinsu da wasu maciya amana Iraniyawa da ke kasashen waje ne suka taimaka musu.

Ayatullah Khamenei ya nanata cewa: Ina fada a fili cewa wadannan tarzoma da rashin tsaro da Amurka da gwamnatin sahyoniyawan mamaya da jabu suka tsara, kuma masu karbar albashi da wasu maciya amana Iraniyawa a kasashen waje ne suka taimaka musu.

Ya kara da cewa: Wasu mutane bisa la'akari da cewa idan aka ce irin wannan lamari da irin ukuwar wani abu tsari da aikin makiya ne, sai su ji wani iri ajikinsu don, kuma suyi kokari wajen kare kungiyar leken asirin Amurka da yahudawan sahyoniya da wasu bayanai , sannan kuma suna amfani da kowane irin nazarce-nazarce da kuma bayanai da ke nuna cewa ba aikin kasashen waje bane.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Akwai tarzoma da dama a duniya, kuma a kasashen Turai musamman a Faransa da Paris ana samun tashe-tashen hankula sau da yawa, amma ko ya taba faruwa ace shugaban Amurka, majalisar Wakilan Amurka su goyi bayan masu tada tarzoma tare da yin bayani akan haka? Shin ya taba faruwa sun aika saƙonni da cewa muna tare da ku? Shin ya taba faruwa kafafen yada labarai da ke da alaka da jari hujjar Amurka da ‘yan amshin shatansu na goyon bayan masu tayar da kayar baya a wadannan kasashe kamar wasu gwamnatocin yankin ciki har da Saudiyya? Kuma ko Shin ya taba faruwa Amurkawa su ba da sanarwar cewa muna da wasu kayan aikin intanet ko software a hannun masu tada kayar baya don ya zamo samu damar sadarwa da juna cikin sauki?.


Ta yaya wadansu ba sa ganin hannun kasashen waje? 

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: To amma irin wannan goyon baya ya sha faruwa a Iran. To ta yaya wasu ba sa ganin hannun waje kuma ta yaya mai hankali ba zai ji cewa akwai wasu hannaye a bayan wadannan abubuwan ba.

Da yake jaddada cewa nuna damuwar dangane da mutuwar wata yarinya da Amurkawa ke yi karya ce kawai, kuma sun nuna sabanin yadda abin yake, suna jin dadi saboda samun wannan uzurin haifar da tarzoma, sun ce: A kasar, jami’an sassan uku sun bayyana nasu jimamin, kuma hukumar shari'a ta yi alkawarin bin lamarin har zuwa karshe domin sanin ko akwai mai laifi ko babu kuma wanene mai laifi? Abin da bincike ke nufi ke nan. Yanzu, ta yaya za a zargi kungiya da tarin ma’aikata kan yiwuwar kuskure. Babu wata dabara a tattare da hakan kuma wannan aikin ba komai bane illa aikin hukumomin leken asiri da masu tsara manufofin kasashen waje.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin da ya gabatar da tambayar, shin mene ne dalilin da ya sa gwamnatocin kasashen waje suke haifar da tarzoma da rashin tsaro a cikin kasar? ya kara da cewa: Suna ganin cewa kasar na samun ci gaba wajen samun madafun iko kuma ba za su iya jurewa wannan lamari ba.

Ayatullah Khamenei ya yi ishara da kara habaka ci gaban kasar a dukkanin bangarori da kuma kokarin bude wasu tsoffin kulli da kuma kunna ayyukan samar da kayayyaki da sansanonin ilimi da kuma yadda kasar za ta iya kawar da takunkumin da aka sanya mata, ya kuma jaddada cewa: ba sa son wadannan ci gaba su samu a cikin ayyukan raya kasa. domin tsaida wannan cigaban sun dauki wannan matakin, na shirya rufe jami'o'i da rashin tsaro a titunan kasar tare da shigar da hukumomi cikin sabbin al'amura a yankin arewa maso yamma da kudu maso gabashin kasar.

Yayin da yake jaddada cewa makiya sun yi kuskure a hasashen da suka yi game da arewa maso yamma da kudu maso gabashin kasar, inda ya ce: Na rayu a cikin al'ummar Baloch kuma suna da matukar biyayya ga tsarin Musulunci. Har ila yau al'ummar Kurdawa suna daya daga cikin al'ummar Iran masu ci gaba kuma suna da sha'awar kasarsu ta asali, Musulunci da kuma tsarin da suke da shi, don haka shirinsu ba zai yi tasiri ba.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi ishara da cewa: tsare-tsare da ayyukan makiya suna nuna halin da suke ciki. Sune makiyan wandanda a cikin maganganun diflomasiyya suka ce ba mu da niyyar mamaye Iran da canza tsarin, sune ke da irin wannan niyya aboye amma kuma suna neman hada baki don haifar da rudani, da lalata tsaron kasar, kuma tada hankalin wasu da zata iya yiwuwa su tada hankulansu sosai.


Shin Suna Neman Iran Ne Ta Zamanin Pahlavi, Wanda Zata Bi Umarninsu Kamar Saniya Mai Shan Nono?

Ayatullah Khamenei ya jaddada cewa, ba wai kawai Amurka tana adawa da Jamhuriyar Musulunci ba ne, har ma tana adawa da Iran mai karfi mai cin gashin kanta, inda ya kara da cewa: Suna neman kasar Iran ta koma zamanin Pahlawi ne, wacce ta ke bi umarninsu kamar yadda saniya mai shan nono ta zamo tana mai bin umarninta.

Ya kara da cewa: Bayan abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, wadannan ‘yan cin zarafi suna nan, kuma fadan ba wai a kan mutuwar yarinya ba ne ko kan kai sanye da hijabi ko rashin sanya hijabi ba. Da yawa daga cikin wadanda ba su sanya cikakken hijabi suna daga cikin masu goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma halartar taruka daban-daban. Yaki da mahawara kan 'yancin kai ne da tsayin daka da karfafawa da kuma ikon Iran din Musulunci ne.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Wadannan mutane da suke aikata fasadi da barna a tituna ba dukkaninsu suke da hukumci daya ba, wasu matasa suna fitowa kan titi saboda kallon wani shiri na intanet da ka gudanar. Irin waɗannan mutane suna iya sanin cewa sun yi kuskure ta hanyar fadakar da su.

Ayatullah Khamenei ya jaddada cewa dukkan wadanda suka fito kan tituna kadan ne idan aka kwatanta da al'ummar Iran da matasa muminai masu kishin addini, yana mai cewa: Tabbas wasu daga cikin wadannan mutanen da suke fitowa kan tituna su ne wadanda suka tsira daga shan kayin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran tayi masu, kamar munafukai, 'yan aware, sarakuna da iyalan Sawaki, ya kamata bangaren shari'a ya tantance irin hukuncin da za a yanke musu, da gwargwadon yadda suke taka rawa a barna da baci ga lumanar kan tituna.

Wani Batu Da Jagoran Juyin Juya Halin Musuluncin Ya Ambata Shi Ne Matsayin Wasu Muhimman Mutane A Farkon Wannan Lamari.

Ayatullah Khamenei ya ce: Da farko wasu kebantattun mutane sun ba da sanarwa da maganganu ba tare da bincike ba, watakila saboda tausayi ne. Wasu daga cikinsu sun zargi hukumar da ke bin doka da oda, wasu kuma na zargin tsarin. Yanzu da suka ga abin da ke faruwa da kuma abin da ya faru a tituna sakamakon kalaman da suka yi da shirin makiya, ya kamata su gyara aikinsu kuma su bayyana karara cewa suna adawa da abin da ya faru na shirin na kasashen waje abokan gaba.

Ya kara da cewa: A lokacin da bangaren siyasar Amurka ke kwatanta wadannan batutuwa da katangar Berlin, ya kamata ku fahimci menene batun, idan kuma ba ku fahimta ba, kun fahimta yanzu kuma ku dauki matsaya.


Al'ummarmu masu fasaha da wasanni suna cikin koshin lafiya kuma kuma masu aminci da mutunci a cikinsu ba yan kadan ba ne, kuma matsayin da wasu 'yan tsirarun mutane suka dauka ba shi da daraja.

Har ila yau Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi ishara da matsayin wasu masana harkokin wasanni da fasaha inda ya ce: A ra'ayina wadannan matsayi ba su da wani muhimmanci kuma bai kamata ya kasance ana kulawa da su ba.

Ayatullah Khamenei ya nanata cewa: Al'ummarmu masu fasaha da wasanni suna cikin koshin lafiya kuma akwai wasu da dama masu imani da daraja a cikinsu, kuma matsayin wasu tsirarun mutane ba shi da wata kima.

Tabbas ya kara da cewa: Ya rage ga bangaren shari'a kan ko matsayinsu na laifi ne ko a'a, amma a dunkule matsayin wadannan mutane ba shi da wata kima, kuma al'ummar fasaha da wasanni ba za su gurbace da wadannan mukamai na 'yan wasa ba. 

A karshen wannan bahasin, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya girmama dukkanin shahidan tafarkin gaskiya da shahidan 'yan sanda da sojoji da kuma shahidan kare tsaro musamman shahidan baya-bayan nan.

A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kira halartar dubban matasa masu kishi da kwazo da himma wajen neman shiga aikin soja a kowace shekara a matsayin wani babban sako kuma mai bishara mai girma da ke dauke da sakon sabon tsarin da cikakken shiri ga kasar, sannan ya kara da cewa: kasancewar matasan Iran a bangarori daban-daban na ilimi, tattalin arziki, siyasa da soja na kasar abu ne mai dauke da matukar fata na kirki.


Yunkurin Samarin Mu Yunkuri Ne Mai Haske A Kowane Fanni

Ayatullah Khamenei kuma yayin da yake ishara da farfagandar bata gari da masu mugun nufi wajen nuna rashin fata, da rashin kima da kuma nuna kyama ga matasan Iran, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewa: hakikanin abin da ya faru shi ne akasin wadannan farfaganda kuma yunkurin samarinmu yunkuri ne mai haske a dukkanin fagage.

A cikin wannan yanayi, ya yi nuni da irin rawar da matasa ke takawa wajen kare kasarsu da tsaron kasar, da taimakawa bangaren gwagwarmaya da yunkurin kare haramin, ayyukan zamantakewa, ci gaban kimiyya, samarwa da kirkire-kirkire, halartar miliyoyin mutane cikin ayyukan ibada kamar gagarumin jerin gwanon Arba'in da jerin gwanon wadanda suka saura, sannan yayi nuni da yanayin yaki da kokarin kariya daga cutar annoba, yunkurin agaji na addini, jihadi ta al'adu da kuma agaji a cikin ibtila’oi na dabiah, sannan ya kara da cewa: wadannan matasa marasa gajiyawa da himma a tsakiyar fagen su ne dai. ba su taba yanke kauna ba kuma ba su yanke alaka da dabi'unsu ba, kuma ba shakka, shugabannin dukkanin wadannan fagage da kungiyoyin sun kasance matasa masu imani.

Babban kwamandan ya kira sojojin kasar a cikin ginshikan jami’an tsaro na kasa tare da jaddada wajabcin karfafa wannan batu, sannan ya bayyana cewa karfafa sojojin yana da muhimmanci biyu ga kasarmu ta Iran, wacce ke fuskantar makiya masu cin zarafi kamar su Amurka, hukumomin soji dole ne su kara karfin tsaron kasar ta hanyar amfani da sabbin hanyoyin warware matsalolin da suka dace, da sanya dukkan shirye-shirye, kayan aiki da kayan aiki mafiya wayo, da karfafa binciken kimiyya, da tsara hadaddun hanyoyin yaki da hadin gwiwar abokan gaba.


Akwai Rashin Tsaro A Manyan Kasashe Kuma Mafi Muninsa A Amurka

Ya kuma kira babban nauyin da ya rataya a wuyan rundunar sojin kasar wajen kare tsaron kasa a matsayin jigo na asali ga al’umma a dukkanin al’amuran rayuwa da suka hada da tsaro a al’amuran kashin kai da tsaro a cikin al’amuran jama’a, ya kuma kara da cewa: idan babu tsaro babu wani ci gaba a kowane fanni.

Ayatullah Khamenei ya kuma kara da cewa, akwai rashin tsaro a manyan kasashe sannan mafi muni a Amurka, kuma a ko da yaushe muna ganin hare-hare a makarantu, shaguna da gidajen cin abinci.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kira sojojin kasar da cewa su ne masu samar da tsaron kasar, yana mai cewa: don haka raunana karfin sojan yana raunana tsaron kasar ne, kuma duk wanda ya kai hari ofishin 'yan sanda ko sansanin Basij ko ya yi wa sojoji ko kuma IRGC batanci a cikin kalamansa, to ya kai hari ne kan tsaron kasar.

Dangane da haka ya kara da cewa: Wajibi ne ‘yan sanda su tashi tsaye wajen tunkarar mai laifi da kuma tabbatar da tsaron al’umma, don haka raunana ‘yan sanda yana nufin karfafa masu laifi ne, duk wanda ya kai hari ga ‘yan sanda, zai kasance ya bar jama’a ba suda masu kare su daga masu laifi, ‘yan daba, barayi. da masu karbar kudi.


Tsaronmu Gaba Daya Yana Cikin Gida Kuma Yana Zaman Kansa Ba Tare Da Dogaro Ga Wasu Ba

Ayatullah Khamenei ya dauki "tsaro na asali" a matsayin wata babbar gata ga kasar inda ya ce: Tsaronmu na cikin gida ne gaba daya ba ya dogara ga waninsa, kuma wannan tsaro ya saba da tsaron da wasu ke samarwa daga waje wanda suna kallon wannan kasa a matsayin wata kasa kamar saniya mai shayar da nono.

Jagoran ya kira tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran da cewa yana tsaye ne sakamakon dogaro da ikon Allah da kuma goyon bayan Imam Wali Asr (AS) da tunani da tsayuwar al'umma da sojojin kasar, sannan ya kara da cewa: Wanda ya dogara ga wani bako, wanda duk ya jingina da wannan runduna ta kasashen waje, to da sannu zasu barshi, saboda me saboda ba za su iya kare shi ba kuma baz asu iya bashi kariya ba.

A cikin wannan taro, Manjo Janar Bagheri, babban hafsan hafsoshin sojojin kasar ya jaddada cewa yunkurin wasu tsirarun mutane da suka gafala ko kuma suka dogara da haifar da rashin tsaro ko shakka babu ba zai kai yunkurin al'ummar Iran masu daraja, kuma ya ce: Sojojin kasar suna tare da jama'a tare da hadin kai da Mutunci wajen aiwatar da umarni kuma dabarun gwagwarmaya za su taka rawa.

Har ila yau, a cikin wannan taro, Admiral II Shafqat, kwamandan zababbun jami’o’in soji, Birgediya Janar Gholami, kwamandan jami’ar Imam Husain, da Birgediya Janar Ahi, kwamandan jami’ar Imam Hassan, sun bayar da rahoto kan tsare-tsaren ayyuka da shirye-shiryen ilimi na wadannan jami’o’in.

Gudanar Da Wakar Hadakar Dalibai Wani Bangare Ne Na Taron Yau.

Bikin yaye sojojin hadin gwiwa wanda aka gudanar a bana a jami’ar Imam Hasan da jami’ar horas da ‘yan sanda ta samu tarba kai tsaye da kuma ta hanyar sadarwar bidiyo a wasu jami’o’in rundunar soji 9, kuma daliban wadannan jami’o’in sun saurari wadannan bayanai na Babban Kwamandan.