6 Janairu 2020 - 05:46
Yan Majalisar Iraqi Sun Amince Da Daftarin Kudurin Neman Ficewar Sojojin Amurka Daga Kasar

A wani zaman na musamman da majalisar dokokin kasar Iraki ta gudanar a yau Lahadi, kimanin yan majalisa 170 ne suka rattaba hannun a daftarin kudirin neman ficewar sojojin Amurka daga kasar, bayan harin Amurka a kasar da ya yi sanadiyar shahadar Janar Qasim Sulaimani kwamandan dakarun Qudus ,da kuma Abu Mahdi Al’ Muhandis mutum na biyu a kungiyar Hashdu’sha’abi ta kasar Iraki.

(ABNA24.com) A wani zaman na musamman da majalisar dokokin kasar Iraki ta gudanar a yau Lahadi, kimanin yan majalisa 170 ne suka rattaba hannun a daftarin kudirin neman ficewar sojojin Amurka daga kasar, bayan harin Amurka a kasar da ya yi sanadiyar shahadar Janar Qasim Sulaimani kwamandan dakarun Qudus ,da kuma Abu Mahdi Al’ Muhandis mutum na biyu a kungiyar Hashdu’sha’abi ta kasar Iraki.

Daftarin kudurin ya kunshi abubuwa guda Ukku , na farko wajibi ne gwamnatin kasar ta yi watsi da duk wani neman taimako daga dakarun hadin guiwa domin yakar kungiyar ta’adda ta Da’ash , domin an kawo karshen yaki a kasar, tun da an yi nasara akan dakarun kungiyar, don haka dole ne gwamnatin ta kori dukkan dakarun kasashen waje da ke kasar.

Kuma dole ne gwamnati da kwamandan hafsoshin sojin kasar su sanar da lokaci da wurin zaman sojojin da ake bukata domin bada horo ga dakarun kasar a Iraki, haka zalika dole ne gwamnati karkashin ma’aikatar harkokin waje ta shigar da kara gaban Kwamitin tsaro na MDD game da keta hurumi da tsaron kasar da Amurka ta yi .

Kuma ana sa ran wannan kuduri zai fara aiki nan take da zarar an amince da shi .


/129