Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: A yayin jawabinsa, Jagora (H) ya bayyana aikin isar da saƙo a matsayin aiki mai muhimmanci, inda ya kawo yadda aikin isar da saƙo a lokacin Manzon Allah (S) ya taimaka wajen yaɗuwar addini. Ya yi bayani kan sauye-sauyen hanyoyin sadarwa da ci gaban da aka samu a wannan zamani, ya bayyana soshiyal midiya a matsayin babbar hanyar isar da saƙo a wannan lokaci.
Jagora (H) ya ja hankali kan muhimmancin kyakkyawan amfani da soshiyal midiya da kuma guje wa zage-zage. Ya ce, “Muna so mu ga sauyi ne a yadda ake amfani da soshiyal midiya.” Ya ƙara da cewa, “Lallai ya kamata a ga bambanci a abin da muke yi da na saura.” Jagora ya kuma ce, “Mu ne ya kamata mu zama malamansu, ya kamata su koya daga gare mu ne.”
A ƙarshe, Jagora (H) ya bayyana hikima, hankali, ilimi da kauce wa zagi da cin mutumci a matsayin hanyoyin da ya kamata a bi wajen isar da saƙo da mu’amala da mutane a soshiyal midiya.
Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
12/Jimadal Akhir/1448
22/11/2026
Ra'ayinka