24 Nuwamba 2026 - 19:28
Source: ABNA24
Larabawan Kasashen Tekun  Farisa Sun Shiga Tsoro Ga Kasadar Netanyahu Kan Iran

Jaridar Isra'ila "Haaretz" ta fallasa cewa ƙasashen Larabawa da ke gefen tekun Farisa suna ganin su ne za su fi shan kashi a duk wani yaƙin da Amurka da Isra'ila za su iya yi kan Iran, don haka suna cikin matuƙar tsoron duk wani rikicin soji. Dangane da sabbin rahotanni, ana sa ran gibin kasafin kuɗin waɗannan ƙasashe zai kai dala biliyan 475.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Tsoron ƙasashen Larabawa na gefen tekun Farisa daga duk wata sabuwar kasadar soji, ya samo asali ne daga mummunan rauninsu na tattalin arziki da Rashin tsaro.

A wannan batun, binciken kamfanin "Allianz Trade" ya nuna cewa waɗannan ƙasashe na iya rasa dala biliyan 790 daga samun tattalin arzikinsu kuma su fuskanci asarar kayan aiki fiye da dala biliyan 200. Wannan kamfani ya nanata cewa idan aka sake fara yaƙi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, waɗannan lahani za su tsananta kuma su ɗauki mafi munin yanayi; al'amarin da ake sa ran zai kai bukatar tare da tanadar kasafin kuɗin waɗannan ƙasashe na dala biliyan 475.

"Ksenia Svetlova," tsohuwar memba ta Knesset (majalisar dokokin) gwamnatin Sahayoniya kuma ƙwararriya kan Gabas ta Tsakiya, dangane da majiyoyi daban-daban a ƙasashen Tekun Farisa ta bayyana cewa waɗannan ƙasashe suna lura da yunkurin Benjamin Netanyahu, firaministan gwamnatin Sahayoniya na tada tashin hankali da Iran kuma suna ƙoƙari da dukkan ƙarfinsu wajen akasin hakan.

Ta tare da yin nuni da cewa Larabawa tun daga farko ba su da sha'awar yaƙi da Iran, ta nanata cewa yanzu ya bayyana cewa su ne za su fi shan kashi a wannan kasada.

Ana gabatar da wannan iƙirarin ne a lokacin da ƙasashen Larabawa na gefen Tekun Farisa suka ba Amurka yawancin sansanonin sojinsu domin a yi amfani da su kan Iran; matakin da ya fuskanci gargaɗin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke maimaitawa cewa za a sami mafi muni hare-hare idan suka sake.

Netanyahu Ba Ya Tunani Kan Ababen More Rayuwar Larabawa

Svetlova a ci gaban nazarinta tare da sukar tsarin Netanyahu ta bayyana: "Idan yanke shawara ta kasance a hannun Netanyahu da kansa, da an fara yaƙi na uku da Iran tun da daɗewa. Ya shafe shekaru yana ɓata lokaci a Gaza, Lebanon, Siriya da Iran kuma yanzu a shirye yake ya yi amfani da kowace hujja don sake fara rikice-rikice domin ya ci gaba da zama kan mulki da kawar da abokan hamayyarsa."

Wannan ƙwararriyar Sahayoniya tare da yin nuni da yarjejeniyoyin Ibrahim ta bayyana: "Ba abin da zai yiwu Netanyahu ya yi tunani ko da na wani lokaci kan wuraren tsarkake ruwa na Saudiyya, ababen more rayuwar mai na UAE ko manyan gidajen zama na Bahrain.

Ya kasance yana rada a kunnen Trump kuma yana ƙoƙarin shawo kan shi da ya kai mummunan hare-hare kan Iran." Ta kwatanta wannan kasada ta soji ga ƙasashen da suka danganta makomarsu da Isra'ila a matsayin "hauka gauraye da wulakanci."

Tsohuwar memba na majalisar dokokin Isra'ila tare da gabatar da wannan tambaya kan "menene zai faru idan dukkan jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami da aka kakkabo su sun sami nasara?" ta amsa cewa sakamakon zai kasance ƙarin samun waɗanda za’a ka kashe da jikkata rna Isra'ila da ƙarin 'yan gudun hijira.

Ta ƙara da cewa: "Masu mulkin ƙasashen Larabawa ba su da sha'awar yaƙi don manufofin siyasa; domin suna gani a fili cewa wani zagaye na hare-hare ba zai kifar da tsarin Iran ba kuma ba zai lalata shirinta na nukiliya ko makamai masu linzami na ballistic ba."

Svetlova a ƙarshe ta nanata cewa a watan Fabrairun 2026, Isra'ila da Amurka sun yanke wata shawara ta masifa kuma nan gaba za ta nuna cewa wannan matakin zai kasance a rubuce a tunanin shugabannin ƙasashen Larabawa waɗanda a yanzu ke tsakanin "guduma ta Iran da magurɗin Isra'ila."

Ta tare da yin nuni da sabanin da ke cikin manufofin Netanyahu ta ce: "An yi nufin hari kan Iran ya zama wani abu na haɗin kai tsakanin Larabawa da Isra'ila, amma a zamanin Netanyahu, wannan kasadar ma kamar sauran shawarwarinsa ya juya zuwa wani abu na rarrabuwa."

..........................

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha