(ABNA24.com) Mai Magana da yawun kungiyar ta Hizbullah a kasar Iraki, ya ce; Amurka tana fada da kungiyoyin kasar Iraki, tana mai amfanin da cewa suna da alaka da Iran, don haka nauyi ne da ya rataya a wuyan al’ummar Iraki su kalubalanci mamayar Iraki.
Kamfanin dillancin labarun “Mehr’ na Iran ya nakalto Muhammad Muhyi yana cewa; Amurkawa suna bayyana Irakawan da su ke fada da Da’esh da cewa ‘yan ta’adda ne kuma yaran Iran ne, sannan ya kara da cewa; Ci gaba da zaman sojojin Amurka a cikin kasar Iraki ba shi da halarci ko kadan.
Kakakin kungiyar ta Hizbullah a kasar Irakin ya kuma ce;; Amurka tana son wawuntar da duniya cewa tana ci gaba da zama ne a cikin Irakin bisa yardar gwmanatin kasar, lamabarin da ba haka yake ba.
A jiya Talata ne dai Irakawa su ka mamaye ofishin jakadancin Amurka a birnin Bagadaza, domin nuna fushinsu akan hare-hare da jiragen Amurka su ka kai wa sansanonin rundunar Hashd assha’abi da ya ci rayukan mutane kusan talatin.
/129
2 Janairu 2020 - 05:34
Lambar labari: 998321
Mai Magana da yawun kungiyar ta Hizbullah a kasar Iraki, ya ce; Amurka tana fada da kungiyoyin kasar Iraki, tana mai amfanin da cewa suna da alaka da Iran, don haka nauyi ne da ya rataya a wuyan al’ummar Iraki su kalubalanci mamayar Iraki.