1 Janairu 2020 - 05:46
Turkiyya Na Kara Matsin Lamba Kan Aikewa Da Sojoji A Libiya

Shugaban kasar Turkiyya ya aike wa majalisar dokokin kasar wani kudirin doka na neman amince masa aikewa da dakaru a kasar Libiya, domin dafawa gwamnatin Tripoli wacce ke fuskantar hare hare daga mayakan dake goyan bayan Janar Khalifa Haftar.

(ABNA24.com) Shugaban kasar Turkiyya ya aike wa majalisar dokokin kasar wani kudirin doka na neman amince masa aikewa da dakaru a kasar Libiya, domin dafawa gwamnatin Tripoli wacce ke fuskantar hare hare daga mayakan dake goyan bayan Janar Khalifa Haftar.

Kudirin dokar wanda shugaba, Recep Tayyip Erdogan, ya sanya wa hannu a aike shi ne ga shuganacin majalisar dokokin kasar, wanda matakin farko ne kafin majalisar ta gudanar da zaman ta na gaggawa a ranar Alhamis domin tattauna batun.

Wannnan dai a cewar kamfanin dilancin labaren Anadolu, na daga cikin yarjejeniyar tsaro da aka cimma a watan Nowamban da ya gabata tsakanin shugaba Erdogan da kuma shugaban gwamnatin hadin kan kasa ta Libiya ta Fayez al-Sarraj dake samun goyan bayan kasashen duniya.

Yarjejeniyar ta tanadi aike wa da sojoji da ‘yan sanda da kuma bada horo.

Kafin hakan dai wani masharcin shugaban kasar ta Turkiyya ya fada a ranar Juma’a data gabata cewa gwamnatin ta Tripoli ce ta bukaci taimakon sojin kasar ta Turkiyya, amma ana bukatar amincewar majalisar dokokin kasar kafin aiwatar da hakan.


/129