28 Disamba 2019 - 06:11
Limamin Juma’a A Tehran Ya Jaddada Wajibcin Riko Da Tattalin Arziki Na Turjiya

Wanda ya jagorancin sallar juma’a a nan birnin Tehran HujatulIslam Kazim Siddiqi ya jadda game da wajibincin dogaro da tsarin tattalin arzki na turjiya domin daidaita alamuran tattalin arziki a fadin kasar,

(ABNA24.com) Wanda ya jagorancin sallar juma’a a nan birnin Tehran HujatulIslam Kazim Siddiqi ya jadda game da wajibincin dogaro da tsarin tattalin arzki na turjiya domin daidaita alamuran tattalin arziki a fadin kasar,

Ya fadi a cikin hudubarsa ta farko cewa jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullahi Sayyid Ali Khamna’I ya jadda game da muhimminanci daukar darasi ga tsarin tattalin arziki da aka yi amfani da shi a shekarar da ta gabata, musamman idan aka yi la’akari da yanayin sabuwar shekarar na yayi daidai da wadda ta gabata ya zama wajabi a yi riko da tattalin arziki na turjiya domin daidaita al’amuran tattalin arziki na kasar,

Ya kara da cewa makiya suna amfani da duk wasu hanyoyin matsin lamba tattalin arziki akanmu , da nufin gurgunta tattalin arzikinta da samar da rashin aikin yi da zaman kashe wando tsakankanin matasa , amma shiryarwa jagora da farkawar Alummar kasa ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin hakar makiya ba ta kai ga ruwa ba,

Daga karshe ya yi Ishara game da tarzomar da ta faru a wasu biranen kasar a baya-bayan nan kan kara farashin manfetur inda ya nuna cewa: Imani, basira da farkawar da al’ummar kasar suka nuna a wancan lokacin wajen tunkarar makiya ya sa aka shallake yanayi mafi muni, da kuma daukar matakai na ganin rikicin bai bazama ba ya shafi zaman lafiya da tsaron kasar,



/129