16 Disamba 2019 - 06:15
Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Sun Kame Palasdinawa Da Dama A Yammacin Kogin Jordan

Majiyar Paladinawa ta ambaci cewa; sojojin HKI sun kame mutane 8 a cikin garuruwa mabanbanta na yankin yammacin kogin Jordan.

(ABNA24.com) Majiyar Paladinawa ta ambaci cewa; sojojin HKI sun kame mutane 8 a cikin garuruwa mabanbanta na yankin yammacin kogin Jordan.

A kusa da wani shingen soja da ke gabashin garin Jenin, ‘yan sahayoniyar sun yi awon gaba da wani matashi, haka nan kuma sun sake kame Usamah Halawah wanda fursuna ne da bai dade da fitowa daga kurkukun HKI ba.

Daga cikin wadanda aka kama din da akwai Shadi Matur, na kungiyar Fatah, da kuma wasu ‘yan gwagwarmaya biyu da su ne Irrin Za’anin da Majid Abu Gazalah a cikin birnin Kudus.

Da akwai dubban palasdinawa da su ke tsare a gidajen kurkukun HKI, da su ka hada da kananan yara 500.



/129