12 Disamba 2019 - 07:57
MDD : Babu Hujjar Cewa Iran Na Da Hannu A Harin Aramko

Masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana cewa ba su samu wani dalili dake tabbatar da cewa kasar Iran nada hanu a harin da aka kai kan ciboyoyin man fetir din Aramko na kasar Saudiya

(ABNA24.com) Masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana cewa ba su samu wani dalili dake tabbatar da cewa kasar Iran nada hanu a harin da aka kai kan ciboyoyin man fetir din Aramko na kasar Saudiya

Cikin wata sanarwa da suka fitar a jiya Talata bayan dawowarsu daga kasar Saudiya, masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun ce ba za su iya amincewa da ikrarin mahukuntan biranan Riyad da Washington ba na cewa Iran ita ce ke da alhakin kai hare-hare kan cibiyoyin man fetir din Aramko mallakin kasar Saudiya.

Tashar talabijin din Bloomberg ta kasar Amurka ta habarta cewa saktare janar na MDD Antonio Guterres ya mika wannan rahoto na watani 6 ga kwamitin tsaro na Majalisar, inda ya tabbatar da cewa Majalisar ta kasa tabbatar da wannan ikirari na kasashen Amurka da Saudiya dake cewa kasar Iran ita ce ke da alhakin hare-haren da aka kai kan cibiyoyin man fetir din Aramko mallakin kasar Saudiya.

A ranar 14 ga watan Satumbar da ta gabata ce jiragen yaki marasa matuka 10 na kasar Yemen suka kai hari kan cibiyoyin man saudiya na Baki'i da Kharis, a matsayin mayar da martani kan hare-haren wuce gona da iri da kawancen saudiyar ke kaiwa kan kasar Yemen. to saidai kasashen Saudiya da Amurka sun zargi kasar Iran da hanu a harin, zargin da mahukuntan jamhoriyar musulinci ta Iran suka sha musantawa.



/129