(ABNA24.com) Shugabar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi ta gurfana a gaban kotun duniya da ke birnin Hague, a Holland, domin kare kasarta daga zargin aikata laifukan kisan kiyashi a kan al'ummar Musulmi, 'yan kabilar Rohingya.
Kasar Gambia ce dai ta shigar da kara a gaban kotun, tana mai nuni da cewa ta dauki wannan mataki ne a matsayinta na kasa mai son ganin an tabbatar da adalci da kare al'ummar ta Rohingya da ta ce hukumomin Myanmar na yi wa kisan kiyashi duk da kasancewarsu 'yan kasar, kuma duniya ta zuba idanu kawai.
A zaman da za a yi na kwana uku, kasar da ta shigar da wannan kara, Gambia da ke yankin Afirka ta Yamma, za ta bayyana dalilanta na bukatar alkalan kotun ta duniya da su hanzarta shiga wannan lamari da ta ce hukumomin Myanmar din na yi wa al'ummarsu ta kabilar Rohingya, wadanda Musulmi ne kisan kiyashi.
Baya ga haka kuma kasar ta Gambia za ta nemi masu shari'ar kotun duniyar da su dauki mataki na ganin hukumomin Myanmar din ba su batar ko lalata duk wata sheda ta aikata laifin na kiyan kiyashi ba a kan al'ummar ta Rohingya da ke lardin Rakhine na kasar ta Myanmar.
/129
11 Disamba 2019 - 05:56
Lambar labari: 992933
Shugabar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi ta gurfana a gaban kotun duniya da ke birnin Hague, a Holland, domin kare kasarta daga zargin aikata laifukan kisan kiyashi a kan al'ummar Musulmi, 'yan kabilar Rohingya.