(ABNA24.com) Mista Macron ya ce ya gayyaci shuwagabannin kasashen kungiyar guda biyar a wani taro ranar 16 ga watan Disamban nan a birnin Pau dake kudancin Faransa.
Makasudin kiran taron a cewarsa shi ne shuwagabannin su fayyace masa ainahin matsayinsu kan kasancewar sojojin faransar a daidai lokacin da kyammar sojojin na faransa ke kara wanzuwa a yankin na sahel.
Macron ya bayyana hakan ne a yayin taron bikin cika shekaru 70 na kungiyar tsaro ta NATO a binin Landan.
Shugaban kasar ta Faransa yana bukata ga shuwagabannin na G5 su fayyace kuma su rubuta bukatarsu ga Faransa da kuma duniya, akan ko suna bukatar kasancewar faransar ko kuma a’a.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan hatsarin jiragen saman faransa masu saukar ungulu guda biyu wanda a yayinsa sojojin na faransa 13 suka mutu a Mali.
A baya baya nan dai an sha gudanar da jerin zanga zanga ta kin jinin ci gaba da kasancewar sojojin faransa a kasashen Mali, Burkina Faso da kuma jamhuriya Nijar.
/129
7 Disamba 2019 - 04:57
Lambar labari: 991803
Shugaban kasar Faransa Emanuel Macron ya Bukaci Shuwagabanin kasashen G5 Sahel dasu fayyace masa matsayinsu kan kasancewar sojojin kasarsa dake jinge a kasashensu.