(ABNA24.com) Ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Mohammad Jawad Zarif ya bayyana cewar wasikar da wasu kasashen Turai uku suka aikawa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya wani kokari ne kawai na rufe gazawar da suka yi wajen cika alkawarin da suka yi cikin yarjejeniyar nukiliya.
Dakta Zarif ya bayyana hakan ne cikin wani sako na Twitter da ya buga a shafinsa inda ya ce wasikar baya-bayan nan da kasashen Turai ukun, wadanda kuma suna daga cikin wadanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar nukiliya da Iran a shekara ta 2015, suka aika wa babban sakataren MDD kan batun makamai masu linzami na Iran wani kokari ne kawai na rufe rashin gazawar da suka yi wajen sauke nauyin da ke wuyansu cikin yarjejeniyar nukiliyan.
Ministan harkokin wajen na Iran har ila yau ya ce idan har wadannan kasashen Turan suna son nuna ikonsu ne kamata yayi su fara da bayyanar da iko da mutumcin da suke da shi ta hanyar kin amincewa da tursasawar da Amurka take musu.
A shekaran jiya Laraba ne dai jakadan kasashen Birtaniyya, Faransa da Jamus suka aika wa babban sakataren MDD wata wasika suna masu ikirarin Iran tana kera makamai masu linzami da za su iya daukar kawukan nukiliya, lamarin da tun da jimawa Iran ta musanta hakan.
/129
7 Disamba 2019 - 04:52
Lambar labari: 991794
Ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Mohammad Jawad Zarif ya bayyana cewar wasikar da wasu kasashen Turai uku suka aikawa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya wani kokari ne kawai na rufe gazawar da suka yi wajen cika alkawarin da suka yi cikin yarjejeniyar nukiliya.