4 Disamba 2019 - 04:21
​MDD Ta Damu Game Da Keta Takunkumin Makamai A Libiya

Kwamitin sulhu na MDD ya bayyana damuwa game da ta'azzarar rikici a Libiya a baya-bayan nan, yana mai kira ga dukkan bangarorin kasar su yayyafawa yanayin ruwan sanyi tare da tsagaita bude wuta.

(ABNA24.com) Kwamitin sulhu na MDD ya bayyana damuwa game da ta'azzarar rikici a Libiya a baya-bayan nan, yana mai kira ga dukkan bangarorin kasar su yayyafawa yanayin ruwan sanyi tare da tsagaita bude wuta.

Mambobin kwamitin sun bayyana damuwarsu ne musamman kan rahotannin keta takunkuman makamai da karuwar shigar dakarun haya cikin rikicin kasar.

Kwamitin ya yi kira ga dukkan kasashe mambobin MDD, su yi cikakkiyar biyayya ga takunkumin makaman, kamar yadda kudurin majalisar na 1970 ya tanada.

Ko baya ga hakan kwamitin ya yi kira ga kasashen da kada su tsoma baki cikin rikicin ko daukar wani mataki da zai iya kara rura wutar rikicin.




/129