3 Disamba 2019 - 04:20
Jami’an Tsaron Iran Sun Kama Mutane 79 Da Ake Zargi Da Hannu Cikin Rikicin Khuzestan

Ma’aikatar tsaron cikin gida da tattaro bayanan sirri ta Iran ta sanar da kama mutane 79 da ake zargi da hannu dumu-dumu cikin rikici da kone-kone da hare-hare da aka kai wasu cibiyoyin gwamnati na baya-bayan nan da suka faru a lardin Khuzestan na kasar Iran.

(ABNA24.com) Ma’aikatar tsaron cikin gida da tattaro bayanan sirri ta Iran ta sanar da kama mutane 79 da ake zargi da hannu dumu-dumu cikin rikici da kone-kone da hare-hare da aka kai wasu cibiyoyin gwamnati na baya-bayan nan da suka faru a lardin Khuzestan na kasar Iran.

Kamfanin dillancin labaran Farsnews na Iran ya nakalto shugaban bangaren yaki da ta’addanci na Ma’aikatar yana cewa: Sakamakon aiki ba dare ba rana da jami’an Ma’aikatar suka gudanar a lardin Khuzestan, sun sami nasarar kame asalin mutanen da suka kai hare-hare kan cibiyoyin gwamnati da na al’umma haka nan da kuma cibiyoyin tsaro yayin rikicin da ya faru a lardin.

Har ila yau sanarwar ta kara da cewa an samu bindigogi 13, tufafin sojojin, lambobin motoci na bogi da sauransu a wajen wadanda aka kama din.

Jami’in ya kara da cewa kungiyoyi uku na ‘yan ta’adda, wadanda suka samu horo daga wata kasa ta makwabta kan yadda za a kai hare-hare kan cibiyoyin tsaro da kuma bude wuta kan jami’an tsaro ne, suka shigo cikin wannan rikici da kuma aikata aika-aikan da aka aikata inda ya ce daga cikin mutanen da aka kama din har da wani dan kasar waje, kamar yadda kuma yace jami’an tsaron sun sami nasarar tarwatsa wasu kungiyoyin ‘yan ta’addan da aka so amfani da su wajen haifar da wannan fitinar.

A makonnin da suka gabata ne dai wasu mutane da suke samun goyon bayan wasu kasashen waje suka yi amfani da jerin gwanon da wasu suka shirya don nuna rashin amincewa da karin farashin mai da aka yi a Iran wajen haifar da fitina da kai hare-hare kan kayayyakin gwamnati da na al’umma, lamarin da yayi sanadiyyar hasarar rayuka da dukiyoyi.




/129